Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dattawa ta amince da kafa kwamitin haɗin gwiwa na wucin gadi (ad hoc) tsakanin Majalisar Dattawa da ta Wakilai domin magance ƙaruwa hare-haren ƙyamar baƙi (ɗenophobia) da ake yi wa ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu.
Rahotanni sun bayyana cewa kwamitin, wanda shugaban Majalisar Tarayya zai jagoranta, zai kai ziyarar bincike da diflomasiyya zuwa Afirka ta Kudu domin nemo mafita mai ɗorewa ga matsalar.
A cikin ayyukansa, ana sa ran tawagar za ta ziyarci majalisar dokokin Afirka ta Kudu domin isar da ƙorafin Nijeriya kan hare-haren da ake kai wa ‘yan ƙasar.
Haka kuma, Majalisar Dattawa na shirin rubuta wasiƙa ga Kakakin Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu tare da gayyatar Ministan Harkokin Waje domin ya yi wa ‘yan majalisa bayani kan sakamakon tattaunawar da aka yi.
Majalisar ta kuma amince da ƙudirin Sanata Simon Lalong na sake duba yarjejeniyar da aka cimma a taron haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu a shekarar 2019, domin tabbatar da an aiwatar da su yadda ya kamata.
A yayin zaman, Sanata Adams Oshiomhole ya gabatar da shawarar soke lasisin kamfanonin Afirka ta Kudu kamar MTN da DSTV a Nijeriya, amma an yi watsi da shawarar bisa dalilan tsarin majalisa.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa ya jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen warware matsalar, yana mai cewa ɗaukar matakin tattalin arziki kan kamfanoni ba shi ne mafita mafi dacewa ba. Ya kuma tabbatar da cewa majalisar na kallon lamarin da muhimmanci tare da ɗaukar matakin gaggawa.
Wannan matsaya ta biyo bayan ƙudirin gaggawa na ƙasa da Sanata Bassey ya gabatar mai taken: “ƙaruwa tsananta hare-haren ƙyamar baƙi ga ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu da Ghana: kira ga matakin gaggawa na ƙasa, diflomasiyya da jin kai domin kare mutunci, tsaro da martabar ‘yan Nijeriya.”
A lokacin muhawarar, ‘yan majalisa sun rarrabu kan ko a mayar da tattaunawar zuwa zaman sirri, bayan da Sanata Aliero ya nemi hakan. Sai dai Sanata Ningi da wasu sun dage cewa a tattauna a fili.
‘Yan majalisar sun nuna damuwa ƙwarai kan hare-haren jiki da kuma yanayin tsoro, matsin lamba na tunani da kuma wulakanci da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a ƙasashen waje. Sun ce ana ƙara ware su da kuma kai musu hari saboda asalinsu na Nijeriya.
fitarDaga ƙarshe, Majalisar Dattawa ta yi shiru na minti ɗaya domin girmama ‘yan Nijeriya da suka rasa rayukansu a irin waɗannan hare-hare a Afirka ta Kudu.
