Daga UMAR GARBA a Katsina
Hukumar Kwastam reshen jihar Katsina ta kama tabar wiwi wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan sha takwas da dubu ɗari ɗaya a watan da ya gabata na Nuwamba.
Muƙaddashin Shugaban hukumar reshen jihar Katsina, Ɗalhatu Wada Chedi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da hukumar ta kira don sanar da jama’a nasarar da ta samu a yaqi da hana shigowa da haramtattun kayayyaki a Nijeriya.
Wada Chedi ya bayyana cewar an kama wasu mutane biyu ne ɗauke da tabar ta wiwi ƙunshi 230 a lokacin da suke ƙoƙarin shigowa da ita cikin jihar Katsina.
Sai dai shugaban hukumar ya ce sun hannata tabar ga hukumar da ke yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi wato NDLEA reshen jihar Katsina don ci gaba da bincike akan lamarin.
Haka zalika hukumar ta kama katan 10 na maganin hana gajiyar jiki wato Diclofenac wanda harajin shi ya kai kimanin Naira miliyan biyar.
Hukumomi da masana daban-daban sun bayyana cewar ƙaruwar shigowa da miyagun ƙwayoyi a jihar ba ya rasa nasaba da ta’ammuli da ‘yan ta’adda ke yi da ƙwayoyin.
“Za mu ci gaba da yin bakin ƙoƙarin mu don ganin an kawo ƙarshen fasa ƙwauri a ƙasar naan,” inji shi.
Daga ƙarshe muƙaddashin shugaban hukumar ya bayyana cewar hukumar Kwastam ba ta nufin gurgunta tattalin arzikin masu shigowa da kaya cikin ƙasar nan sai dai tana roƙonsu da su kasance masu bin dokokin gwamnati don ganin suna shigowa da kaya ta hanyar da doka ta amince.