Kwastom ta kama naman jaki na miliyoyin Naira a Kebbi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jami’an Hukumar Kwastam a jihar Kebbi sun ce sun kama naman jaki 180 da ake yunƙurin yin fasa-ƙwaurinsa.

Kwamandan rundunar a jihar Kebbi, Iheanacho Ojike, shi ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce sauran kayaki da suka kwace sun haɗa da litar man fetur har guda 16,300 da tufafi da kuma katan-katan guda 74 na wasu magunduna daban-daban wanda kuɗin fitonsu ya kai sama da naira miliyan 300.

Iheanacho ya ce an yi samu nasarar kama kayan ne bisa irin ƙoƙari da jami’an hukumar suke yi wajen kakkaɓe masu aikata ɓarna.

Kwamandan hukumar ya ce wasu mutane na amfani da lokacin tsadar man fetur wajen safararsa zuwa waje.

Ya ƙara da cewa, an kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a fasa kwaurin kayakin.

Ya kuma gargaɗi masu fasa kwauri da su daina domin jami’ansu a shirye suke wajen cafke su.