Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Yayin da aka rage amfanu da man fetur a faɗin Nijeirya sakamakon tashin farashinsa, ’yan kasuwar sun nuna damuwarsu kan yadda suke tafka asara, inda kusan dillalan mai 10,000 ke shirin rufewa kasuwarsu.
Alƙaluma daga hukumar kula da man fetur ta Nijeriya na nuna cewa yawan amfani da man fetur ya ragu zuwa lita miliyan 4.5 a kowace rana a watan Agustan 2024, ya ragu daga lita miliyan 60 a kowace rana a watan Mayun 2023 – wanda ya ragu da kashi 92 cikin ɗari.
Bayanai sun kuma nuna cewa jihohi 16 ne kawai daga cikin 36 ɗin suka samu man fetur daga kamfanin mai na Nijeriya a watan Agusta, lamarin da ya janyo ƙarancin man.
Tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, farashin man fetur ya tashi da kusan kashi 488 cikin 100, inda ya tashi daga N175 zuwa sama da N1,000 a watan Oktoban 2024.
ƙarin farashin da ake ci gaba da fuskanta ya kawo taɓarɓarewar tattalin arziki, tare da ƙara tsadar sufuri da kuma ƙara haɓaka hauhawar farashin kayayyaki, yayin da ‘yan Nijeriya ke kokawa kan halin ƙunci. Lamarin ya kuma tilastawa masu ababen hawa da yawa barin motocinsu, inda suka zaɓi amfani motocin haya.
Shugaban ƙungiyar masu sayar da man fetur a Njjeriya, ya ce raguwar yawan amfani da man da aka samu ya janyo wa ƙungiyar asara mai yawa, inda ya ce kimanin mambobinsa dubu 10 ne ke daf da rufewa.
Da yake magana da wannan manema labarai, jami’in hulɗa da jama’a na PETROAN na aasa, Dokta Joseph Obele, ya ce farashin tirelar man fetur ya tashi daga Naira Miliyan 7 zuwa Naira Miliyan 47 a cikin watanni 16 da suka gabata.