
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kwastom (NCS), ta bayyana rahoton ƙara wa’adin Kwantirola-Janar, Bashir Adewale Adeniyi a matsayin ƙarya da kuma abinda ake yaɗawa don ƙoƙarin ruɗar da al’umma.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ta hannun jami’inta na hulɗa da jama’a, Abdullahi Maiwada, NCS ta ce, naɗe-naɗe ko ƙara wa’adin Kwantirola-Janar na Kwastom, iko ne na Shugaban ƙasa kaɗai ba ga wani ko wata hukuma ba.
Ya kuma ce, za a yi hakan ne a ƙarƙashin dokar NCS ta 2023 da wasu dokoki da ke gudanar da tsare-tsaren naɗa muƙamai, ya na mai cewa babu wani umarni daga hukumomin da ke da alhakin yin hakan ga NCS.
Ya ƙara da cewa, rahoton ba zai samar da tsaiko ga jagoran hukumar ba wajen yin ayyukan da suka dace da ƙoƙarin kawo ci-gaba a yayin sauke nauyin da aka ɗora masa.
Don haka ne NCS ta ce lallai rahoton ba gaskiya bane, ta na mai kira ga al’umma da su ƙaurace masa.
