
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Galadiman Kano kuma ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki, Alhaji Abbas Sanusi.
Marigayin ya rasu ya na da shekaru 92 a duniya bayan fama da wani dogon rashin lafiya.
Ya rasu ya bar ƴaƴa da dama da jikoki, kamar yadda Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana, ranar Laraba.
Daga cikin ƴaƴan nasa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, wanda shi ne shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano.
Shugaba Tinubu ya bayyana Galadiman a matsayin ginshiƙi daga cikin ginshiƙan al’adun gargajiya, wanda ya bada gagarumar gudummawa ga masarautar Kano da jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga gwamantin Kano da Majalisar Masarautar Kano da kuma al’ummar jihar, tare da yi masa addu’ar fatan samun rahamar Allah SWT.
