Gwamna Abba, Sarki Sunusi, Barau, Kwankwaso sun halarci jana’izar Galadiman Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabiru Yusuf, da mataimakinsa Kwamred Aminu Abdussalam, da Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi II da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin sun halarci jana’izar Marigayi Galadiman Kano Abbas Sunusi.

Babban Limamin Kano Farfesa Sani Zahradden, ne ya jagoranci gudanar da sallar Marigayi Galadiman na Kano Abbas Sunusi, wanda aka gudanar a ƙofar Kudu, fadar Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi II.

Galadiman Kano Abbas Sunusi ya rasu yana da shekaru 91 a duniya, kuma kawu ne ga sarki Muhammadu Sunusi II, kuma mahaifi ga shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas.

Kazalika, tsohon gwaman Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Abdullahi Abbas shugaban APC na Kano da shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Jibril Ismail Falgore da sauran al’umma da dama suna daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar.

Marigayin dai shi ne Wamban Kano babban ɗan majalisar sarki kafin ɗaga likkafar sarautarsa zuwa Galadiman Kano, wanda tun a shekarun 1950 Abbas Sanusi ya zama mamba a majalisar Masarautar Kano, inda a karon farko mahaifinsa, Sarki Sanusi I, ya naɗa masa rawanin Sarkin Dawakin Tsakar Gida kuma hakimin Ungogo a shekarar 1959.

Tuni dai aka binne Marigayi Galadiman Kano Abbas Sunusi a maƙabartar Gandun Albasa da ke nan Kano.

A lokacin mulkin Sarki Muhammadu Sunusi II ne dai aka ɗaga likafarsa zuwa Galadiman Kano. An dai haifi Abbas Sanusi a shekarar 1933 a garin Bichi da ke nan Jihar Kano, ya rasu yana da mata da ƴaƴa 35.

By ukarofi