Ƙungiyar NUJ ta Zamfara ta yaba wa Gwamna Dauda bisa alƙawarin gina sakatariyar ƙungiyar

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙungiyar ‘yan jarida reshen Jihar Zamfara ta yaba wa gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal bisa alƙawarin sake gina sakatariyar ƙungiyar ta zamani da ke Gusau babban birnin jihar.

Shugaban ƙungiyar na jiha, Kwamared Ibrahim Musa Maizare ya yi wannan yabon a wata hira da manema labarai a Gusau a yau Laraba.

A cewarsa, yabon ya zama wajibi bisa la’akari da damuwar da Gwamna Dauda Lawal ya nuna ga ƙungiyar da ɗaukacin ‘yan jarida masu aiki a jihar.

Kwamared Maizare ya bayyana cewa yanayin da ginin sakatariyar yake ciki na fuskantar barazanar rugujewa.

“Dukkan gine-ginen da muke da su a sakatariyar NUJ ta jihar, tun daga rukunin shagunan ta, katanga da ofisoshi sun lalace sama da shekaru 20 da suka wuce, kuma muna godiya ga gwamnan jihar Dauda Lawal bisa taimakon gaggawa da ya yi na sake gina sakatariyar tamu”. Yace

Ya ce idan aka sake gina sakatariyar, zai baiwa ‘yan jarida masu aiki a jihar damar yin aiki cikin sauƙi.

Ya yi alƙawarin cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bai wa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal goyon baya domin samun nasarar ta.

“Muna matuƙar farin ciki kuma mun gamsu da damuwar da Gwamna Dauda Lawal ya nuna wa NUJ a Zamfara kuma a shirye muke mu ba gwamnatinsa goyon baya don samun nasara da ci gabanta”. Yace

Kwamared Maizare ya buƙaci ’yan jarida a jihar da su riƙa aiki bisa ƙa’idojin aikin jarida tare da marawa gwamnati baya a dukkan matakai domin ci gaban Zamfara da ƙasa baki ɗaya .

By ukarofi