
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yaba wa ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Monday Okpebholo na Edo bisa nuna kaɗuwarsu game da iftila’in da ya yi sanadin kisan mafarauta 16 a garin Udene na Ƙaramar Hukumar Uromi a Jihar Edo.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kwamishinan Labarai na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, Gwamna Abba ya bayyana alhininsa kan lamarin inda ya jaddada kira da a tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda aka rasa da waɗanda suka samu raunuka.
Ya ce, lallai akwai buƙatar ɗaukar matakin doka da gabatar da masu laifi a lamarin a bainar jama’a don tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa an yi adalci.
Ya kuma yaba wa Gwamna Okpebholo bisa haɗa kai da al’ummar Hausawa na Edo don ƙaurace wa faruwar irin haka a nan gaba da kuma ƙoƙarin biyan diyya ga iyalan waɗanda aka rasa.
Bugu da ƙari, Gwamnatin Kano ta yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan gaggauta umartar hukumomin tsaro su kamo waɗanda ke da hannu a laifin tare da tabbatar da sun fuskanci hukuncim doka.
Ya bayyana hakan a matsayin ƙoƙarin Gwamantin Tarayya ga harakar tsaro da bada kariya ga ƴan Nijeriya ba tare da nuna wariya ba.
Haka kuma, al’ummar Torankawa inda nan ne garin galibin waɗanda iftila’in ya rutsa da su, sun yaba da hoɓɓasa da Gwamnatocin Edo da na Tarayya suka yi wajen kula da al’amarin, ganin yadda suke ƙoƙarin tabbatar da adalci.
