Kwastom ta Nijeriya ta yi murnar samun mace ta farko matuƙiyar jirgi a Amurka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta bayyana farin ciki da jin daɗi bayan wata jami’arta, Sufurintandan Kwastom Nafisat Balogun, ta samu gagarumar nasara ta zama mace ta farko a cikin hukumar da ta mallaki lasisin tuƙin jirgi na kasuwanci mai injina da dama daga ƙasar Amurka.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdullahi Maiwada, ya fitar a ranar Litinin, ya ce an gudanar da wani biki na musamman domin karrama Balogun, wanda Sashen Fasaha na Kwastom ya shirya, tare da halartar manyan jami’ai, shugabanni da abokan aiki.

Sanarwar ta bayyana wannan nasara a matsayin tarihi mai muhimmanci, inda Balogun ta zama mace ta farko matuƙiyar jirgi a tarihin Hukumar Kwastom, wani fanni da a baya ya kasance ƙarƙashin rinjayar maza.

Da yake jawabi a wajen bikin, Manajan Darakta na Sashen Fasaha na Kwastom, Kwamandan Kwastom (mai ritaya), Kyaftin Kuhi Mbaya, ya bayyana tafiyar Balogun a matsayin abin koyi da kuma abin alfahari.

Ya ce, “Jami’armu Nafisat Balogun ta fara daga aikin kula da fasinjoji a jirgi, zuwa zama cikakkiyar matuƙiyar jirgin kasuwanci. Wannan babbar nasara ce ba gare ta kaɗai ba, har ma ga dukkanin hukumar.”

Mbaya ya jaddada cewa wannan nasara ta kafa sabon tarihi, tare da nuna yadda dama ke ƙaruwa a cikin hukumar.

“Yanzu a karon farko muna da mace matuƙiyar jirgi a cikin Kwastom. Ta kafa tarihi, kuma ya zama wajibi mu yi bikin wannan gagarumar nasara,” inji shi.

Ya kuma ƙarfafa gwiwar mata da su bi burinsu ba tare da tsoro ba, yana mai cewa an riga an karya shingen da ke hana mata shiga wasu fannoni.

“Wannan nasara na nuna cewa babu abin da ya gagara. An karya shingen da ke hana mata kai wa ƙololuwa, kuma da jajircewa da ƙwazo, mata za su iya cimma burinsu,” inji Mbaya.

Har ila yau, ya yaba wa Shugaban Hukumar Kwastom, Kwanturola-Janar Adewale Adeniyi, bisa jagoranci da goyon bayan da yake bai wa shigar mata cikin ayyukan hukumar.

A nata ɓangaren, Sufurintandan Kwastom (Matuƙiyar Jirgi) Nafisat Balogun ta nuna godiya matuƙa bisa wannan karramawa da kuma goyon bayan da ta samu daga shugabanni da abokan aiki.

Ta ce, “Ina matuƙar godiya da wannan tarba mai cike da karamci. Tafiyata ba ta kasance mai sauƙi ba, amma ina gode wa dukkan waɗanda suka ba ni goyon baya da ƙarfafa gwiwa.”

Ta kuma bayyana cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon tallafin da shugabancin hukumar ya bayar.

“Na gode ƙwarai ga Kwanturola-Janar da dukkanin shugabannin hukumar bisa wannan gagarumin goyon baya. Wannan nasara shaida ce ta irin wannan ƙarfafawa,” inji ta.

Balogun ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki da ƙwazo da gaskiya, tare da ɗaga darajar hukumar.

“Na yi alƙawarin ci gaba da aiki da sadaukarwa, gaskiya da ƙwarewa domin ɗaukaka sunan hukumar,” inji ta.

Sanarwar ta ƙara da cewa, abokan aikinta da suka halarci bikin sun nuna farin ciki da alfahari da wannan nasara, inda suka bayyana ta a matsayin abin ƙarfafa gwiwa ga sauran jami’ai, musamman mata, domin su ƙara ƙoƙari wajen neman ilimi da ƙwarewa a fannoni na musamman.

By ukarofi