Bayyanar Minista Musawa sanye da ɓangwalelen tabarau ya haddasa muhawara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministar Harkokin Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin ƙirƙire-ƙirƙire ta ƙasa, Hannatu Musa Musawa, ta janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan ta halarci wani taron jama’a sanye da tabarau mai tsada, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi tsakanin ’yan Nijeriya.

Ministar ta wakilci Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a bikin kamun kifi na Nwonyo na shekarar 2026 da aka gudanar a tafkin Lake Nwonyo, cikin ƙaramar hukumar Ibi a jihar Taraba.

Bikin ya ja hankalin baƙi da masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na ƙasa da ma ƙasashen waje.

Da take bayyana ra’ayinta kan bikin a shafinta na ɗ, Musawa ta ce taron wata babbar dama ce ta nuna al’adun Nijeriya da kuma bunƙasa tattalin arziki ta hanyar yawon buɗe ido. Ta yabawa gwamnan jihar, Agbu Kefas, bisa farfaɗo da bikin bayan shafe shekaru 14 ba a gudanar da shi ba, tana mai cewa hakan alama ce ta haɗin kai da kuma juriya na al’ummar yankin.

Sai dai duk da wannan yabo, hankalin jama’a ya fi karkata ne kan tabarau da ministar ta sanya, wazanda aka gano suna daga cikin nau’in Gucci GG1244S-001 sunglasses da kuma Gucci GG0541S sunglasses.

Rahotanni daga shagunan intanet sun nuna cewa farashin tabarau irin wannan na kaiwa tsakanin Yuro 590 zuwa 780, wato kusan dubban Naira ɗari bakwai zuwa sama da miliyan ɗaya, gwargwadon kasuwa da wurin saye.

Wannan lamari ya haifar da muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, inda wasu suka soki ministar kan amfani da kayan alatu a lokacin da jama’a ke fama da matsin tattalin arziki. Wasu kuwa sun kare ta, suna cewa matsayin ta da tarihinta a rayuwa ya ba ta damar amfani da irin waɗannan kayayyaki ba tare da alaƙa da kuɗin gwamnati ba.

Masu sharhi na ganin cewa irin wannan muhawara na nuna yadda jama’a ke ƙara sa ido kan rayuwar shugabanni da jami’an gwamnati, musamman a lokutan da tattalin arziki ke fuskantar ƙalubale. Duk da ce-ce-ku-cen, bikin ya ci gaba da zama wata muhimmiyar hanya ta nuna al’adun Nujeriya da kuma jan hankalin duniya.

A ƙarshe, wannan lamari ya sake tayar da tambaya kan iyaka tsakanin rayuwar kai da kuma matsayin jama’a ga jami’an gwamnati, tare da nuna cewa duk wani abu da shugabanni suka yi na iya zama abin muhawara a idanun al’umma.

By ukarofi