Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Ministan Sufuri na Nijeriya, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, tare da matarsa Patience Jonathan, su ne suka tilasta masa ficewa daga jam’iyyar PDP.
Amaechi ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a shirin talbijin na The Morning Brief a tashar Channels, inda ya ce an karɓe masa tsarin siyasa a jihar Ribas, lamarin da ya sa aka kore shi daga jam’iyyar.
A cewarsa, “an tilasta mini fita daga PDP… shugaban ƙasa da matarsa sun karɓe tsarin siyasa a Ribas, suka hana ni damar cigaba.” Ya ƙara da cewa irin wannan lamari ya sake faruwa da shi a cikin jam’iyyar APC.
Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya jaddada cewa ya fuskanci rashin adalci a jam’iyyun biyu, yana mai cewa ba zai taɓa yin shiru ba idan aka aikata rashin gaskiya. “Duk lokacin da na yi magana kan rashin adalci, sai a fara ƙoƙarin kawar da ni daga tasiri,” inji shi.
Amaechi ya bar PDP a shekarar 2013 bayan dakatar da shi bisa zargin aikata abin da ya saɓa wa dokokin jam’iyya. Daga bisani kuma ya fice daga APC a shekarar 2025, inda ya soki shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ba zai iya tafiyar da ƙasar yadda ya kamata ba.
A ɓangaren siyasar gaba, jigo a jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa zai mara wa tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar baya idan ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.
Sai dai ya yi nuni da cewa dole ne a yi la’akari da shekaru da ƙarfi wajen shugabanci, duk da cewa Atiku na da cancantar tsayawa takara. Haka kuma, Amaechi ya ƙi amincewa da batun rabon mulki bisa yankuna, yana mai cewa cancanta ce kaɗai ya kamata ta zama ma’auni wajen zaɓen shugabanni.
Ya ce, “ba na goyon bayan raba mulki tsakanin Arewa da Kudu. Abin da na yi imani da shi shi ne a bai wa mafi cancanta damar shugabanci.”
Rahotanni na nuna cewa kalaman Amaechi na ƙara ɗaga hankali a fagen siyasar Nijeriya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027, inda ake ci gaba da muhawara kan shugabanci, adalci da kuma tsarin dimokuraɗiyya.
