Layikan waya a ƙananan hukumomin Katsina bakwai za su cigaba da kasancewa a rufe – Masari

Daga SANI AHMAD GIWA

Gwamnatin Jihar Katsina ta bada sanarwar cewa ƙananan hukumomi 7 daga cikin 17 da gwamnatin jihar ta katse wa layukan sadarwa a ƙoƙarin ta na magance matsalar tsaron da ta addabi jihar, za su ci gaba da zama a rufe.

Hakan ya fito ne daga bakin Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamna Masari, Alhaji Abdu Labaran a ranar Juma’ar nan.

“Gwamna Masari ya rubuta wa Kamfanin da ke Kula da Harkokin Sadarwa na Nijeriya (NCC) takardar neman buƙatar a maido da hanyoyin sadarwar ƙananan hukumomi 10 daga cikin 17 da aka katse wa layuka fiye da wata uku da suka wuce.

“Daga cikin qananan hukumomi guda goman akwai: Kurfi, Dutsinma, Matazu, Musawa, Malumfashi, Ɗandume, Bakori, Funtua, Ƙafur da kuma Ɗanja.

“Sauran ƙananan hukumomin Faskari, Sabuwa, Batsari, Safana, Ƙanƙara, Ɗanmusa da kuma Jibiya, za su ci gaba da kasancewa babu sadarwa,’ inji shi.

Ya sake bayyana cewa gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki ƙwararan matakai da saka doka don shawo kan matsalar tsaro a jihar, inda ta katse layukan sadarwa a ƙananan hukumomi 17.

A cewar sa, dokar ta kuma bada umarnin dakatar da yin amfani da wasu hanyoyi a yankunan da suke fama da matsalar tsaro tare da yin safarar itace a faɗin jihar.

“Hana sana’ar dabbobi da kuma rufe manyan kasuwanni a yankin da matsalar ta shafa da kuma saye ko sayar da babura a kasuwannin yankin.

“Haka kuma dokar ta hana sana’ar acava da Keke Napep daga ƙarfe 10 na dare zuwa 5:30 na asuba a duk faɗin jihar.

Ya ce gwamnatin ta yanke wannan shawara ne bayan lura da ta yi cewa an samu sauƙin ayyukan ta’addanci a jihar da kuma hidimar masu ba wa ’yan ta’addan wasu bayanai.

A cewarsa, da ma gwamnatin ta rufe layukan sadarwa ne a matsayin matakin wucin-gadi da nufin daƙile ayyukan ta’addanci da masu taimaka wa ’yan ta’adda a faɗin jihar, musamman a tsakanin waɗannan hukumomin 17 da ‘yan bindigar dajin da ake zargin ɓarayin shanu da yin garkuwa da mutane tare da kisan ba gaira ke kaiwa ke cin karensu babu babbaka.