
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumomin tsaro sun yi nasarar cafke waɗansu mutane biyu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne a Jihar Legas, lamarin da ya sake tayar da hankula kan yiwuwar faɗaɗar ayyukan ta’addanci zuwa kudancin Najeriya daga Arewa maso Gabas.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) ne suka kama wani mai suna Modu Gana da Ibrahim Dugge a safiyar ranar Lahadi a garin Apapa, inda kuma tuni suka garzaya da su ofishinsu domin gudanar da bincike akansu.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, atisayen ya samo asali ne daga sahihan bayanan sirri, kodayake ba a bayyana dalla-dalla yanayin da ya kai ga yin nasarar kamen ba.
Majiyoyin na zargin cewa mutanen biyu sun iya tserewa ne daga yankin arewa maso gabas sakamakon matsin lambar sojoji akan ƴan ISWAP da Boko Haram, inda rikicin ya shafe sama da shekaru 15 yana haddasa asarar rayuka da ɗaiɗaita al’umma.
Kawo yanzu hukumomi ba su bayyana manufar zuwansu Legas ba, sannan masana tsaro sun yi gargadin cewa ƙungiyoyin masu tsatstsauran ra’ayi na ƙara ƙoƙarin kafa sansanonin ɓoye da hanyoyin tallafi a waje da yankunan da aka saba danganta su da su, musamman a manyan birane, lamarin da za a iya kira da sauya dabarun ayyukansu a sassan ƙasar.
