Katsina za ta samu masu kula da lafiya na tsawon sa’o’i 24 a dukkan unguwanni

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Akan haka ne gwamnan jihar Malam Dikko Raɗɗa ya amince da sayen motocin ɗaukar marasa lafiya 15, da babura masu ɗaukar marasa lafiya 102.

Motocin masu cikakken kaya za su ƙarfafa ayyukan bayar da agajin gaggawa a faɗin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake duba aikin haɗa baburan ɗaukar marasa lafiya a ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarauta ta Jihar Katsina.

Gwamna Raɗɗa ya ce wannan shiri yana nuna ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da cewa dukkanin unguwanni 361 na Jihar Katsina suna da damar samun kulawar lafiya ta gaggawa.
“Mun yi alƙawari cewa kowanne unguwa zai amfana da wannan shiri, kuma ina matuƙar farin ciki da irin ci gaban da aka samu zuwa yanzu,” inji malam Dikko.

Ya bayyana cewa an kammala baburan ɗaukar marasa lafiya guda 102, yayin da ake ci gaba da aiki kan sauran, yana mai cewa aikin na tafiya a hankali zuwa kammalawa gaba ɗaya.

“Abin da muka gani a yau ya nuna gagarumin ci gaba, kuma mun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa an rufe dukkanin unguwanni gaba ɗaya,” in ji Gwamna Raɗɗa.

Ya sanar da cewa zuwa shekarar 2026, dukkanin baburan ɗaukar marasa lafiya za su kasance a shirye, tare da tabbatar da cewa kowane unguwa na da aƙalla cibiyar kula da lafiya ta matakin farko (PHC) guda ɗaya da ke aiki na sa’o’i 24 a kowace rana, tare da tallafin motocin ɗaukar marasa lafiya da kayan gwaji na asali.

Gwamnan ya bayyana cewa baburan ɗaukar marasa lafiyar za su kasance na tura marasa lafiya (referral), wato ɗaukar marasa lafiya daga cibiyoyin lafiya na farko zuwa manyan asibitoci, musamman a karkara da wuraren da ke da wahalar isa.

Ya ƙara da cewa kowanne babur na ɗauke da tankin iskar oxygen, gadon mara lafiya, da muhimman kayan taimakon farko domin tallafawa ayyukan jinya na gaggawa.

“Wannan shiri na nufin ceton rayuka ne, shi ya sa muke ɗaukar sa da muhimmanci sosai,” in ji shi.

Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa sabbin motocin ɗaukar marasa lafiya na zamani guda 15 da aka amince da su za a jibge su a manyan hanyoyi a faɗin jihar domin bayar da agaji cikin gaggawa ga haɗurra mota da sauran matsalolin gaggawa.

“Da kiran waya guda, ya kamata motar ɗaukar marasa lafiya ta iso cikin mintuna biyar zuwa goma domin ɗaukar waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti mafi kusa,” in ji gwamnan.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar na zuba jari a motocin ɗaukar marasa lafiya masu inganci da cikakken kayan aiki domin ƙarfafa tsarin kula da lafiya na gaggawa da rage nauyi a kan manyan asibitoci na sakandare.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na ɗaukar ma’aikatan lafiya a halin yanzu domin cike giɓin ma’aikata da kuma tallafawa shirin aiki na sa’o’i 24 a cibiyoyin lafiya na farko.

“Ba za ka iya gudanar da cibiyar lafiya na sa’o’i 24 ba tare da isassun ma’aikata ba. Shi ya sa muke ci gaba da ɗaukar ma’aikata,” in ji shi.

Gwamna Raɗɗa ya sake jaddada cewa lafiya, ilimi da noma su ne manyan abubuwan da gwamnatinsa ta bai wa fifiko, yana mai bayyana kula da lafiya a matsayin ginshiƙi na samar da aiki da ci gaba.

Ya yabawa ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarauta bisa jajircewarta wajen aiwatar da aikin, tare da godiya ga goyon bayan jami’an ƙananan hukumomi.

By ukarofi