
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ce hukumomin tsaron Nijeriya suna aiki da kamfanonin kafafen sada zumunta domin ganowa da kuma soke shafukan da ƴan ta’adda da ƙungiyoyinsu ke amfani da su wajen tallata ayyukansu da tara kuɗaɗe.
Da yake jawabi yayin isar da saƙon ƙarshen shekara a Abuja ranar Talata, Darakta Janar na Cibiyar yaƙi da ayyukan ta’addanci, Manjo Janar Adamu Laka, ya ce kafofi irin su TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X ƴan ta’adda suke amfani da su wajen yaɗa manufofinsu da ayyukansu gami hulɗa da masu taimaka musu.
Ya ce, hukumomin tsaro sun yi zama akan al’amarin a lokuta da dama da kamfanonin kafafen domin warware saƙonnin da suke wallafawa da ke barazanar ga zaman lafiyar ƙasa.
Ya bayyana cewa, sun yi nasarar daƙile shafukan wasu bidiyoyi da ƴan bindiga ke amfada su wajen nuna kuɗaɗen fansa ko kuma ta tattaunawa ta kai-tsaye.
Shugaban sojojin ya ƙara da cewa, dabarun ƴan ta’adda na ƙaruwa ciki har da amfani da masu taimaka musu da shafukan da ba a tantance ba, yana mai cewa akan haka hukumomin tsaro suke aiki tuƙuru wajen garin sun daƙile dukkan salon da suka ɓullo da su.
A cewarsa, tura kuɗaɗen fansa ta na’urorin POS waɗanda da su ƴan bindiga ke samun kuɗaɗen shiga, ya taimaka wajen bada matsala ga ayyukan bin diddigi da jami’an tsaro suke yi na farauto su.
