Likitoci sun cire idon mara lafiya bisa kuskure yayin tiyata

Spread the love

Likitoci da ke aikin tiyata a wani babban asibitocin ƙasar Sloɓakia sun cire lafiyayyen idon wani mara lafiya a maimakon mara lafiyar yayin wata tiyata, inda a yanzu ya koma makaho gaba ɗaya.

Kamfanin Dillancin Labarai na TARS ne ya rawaito hakan a makon da ya gabata.

Sai dai rahotanni sun ce tuni likitan, wanda ke aiki da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bratislaɓa, da ya aikata katoɓarar ya cika wandonsa da iska.

Asibitin dai a sakamakon haka ya zaunar da iyalan mutumin domin ba su shawarwari domin su rage raɗaɗin halin da aka jefa su a ciki.

A cewar TARS, tuni hukumomin lafiyar ƙasar suka fara gudanar da bincike don gano yadda aka yi ma lamarin ya faru tun da farko.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da ɓangaren lafiyar ƙasar ta Sloɓakia ke fama da yajin aiki.

Ko a makon da ya gabata sai da ƙungiyar Likitoci ta ƙasar (LOC) ta ce, akwai mambobinta kimanin 3,000 da suke a shirye su ajiye aikinsu matuƙar ba a yi musu ƙarin albashi tare da inganta yanayin aikinsu ba.

ƙasar dai na fama da kamfar likitoci inda suke fice wa zuwa ƙasashen waje, musamman Jamhuriyar Czech da Austria, kuma annobar Korona ta dada ta’azzara lamarin.

By ukarofi