Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe

Spread the love

’Yan sanda sun fara farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya yi wa matarsa kisan gilla da adda a garin Babbangida da ke ƙaramar Hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a kauyen Koriyel.

“Ya aikata hakan ga matarsa ’yar shekaru 40 ta hayar amfani da adda, inda ya kashe ta ya kuma tsere saboda wasu dalilai da har yanzu ba a tantance ba,” inji sanarwar.

Tuni dai ’yan sanda suka fara ƙoƙarin cafke wanda ake zargin domin ya fuskanci shari’a.

A wani labarin kuma, ’yan sanda sun kama wasu mutane biyu da kasa zargin sun kashe wani mutum bisa zargin satar waya a garin Ngalda da ke ƙaramar Hukumar Fika.

“An zarge su ne da laifin kashe wani bisa zargin da da satar wayar hannu da na’urar cajin waya, kima dukkansu sun amince da aikata laifin kuma suna fuskantar bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar,” inji shi.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya buƙaci mazauna yankin da su nemi hanyoyin warware rigingimu cikin lumana, su guji ɗaukar doka a hannunsu.

By ukarofi