Tarihin rayuwar Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An haifi Aminu Ɗantata a ranar 19 ga watan Mayun 1931, daga gidan ɗantata a Kano. Mahaifinsa shi ne Alhaji Alhassan Ɗantata, ya kasance shahararren attajiri a duk yankin Yammacin Afirka a farkon ƙarni na 20.

Ɗantata bai gaji dukiya kaɗai daga mahaifinsa ba, ya gaji ɗabi’u, karamci da kamun kai. Duk da irin arziƙinsa, Alhassan Dantata bai yarda da nuna kai ko karɓar sarauta ba.

Ya gina rayuwa mai kyau da aminci, wanda ya bai wa ‘ya’yansa damar girma cikin ƙima da kuma tasowa cikin natsuwa.

Wannan ne ya sa Aminu, tare da jikan ɗan uwansa Aliko Dangote, wanda a yanzu shi ne attajiri mafi kuɗi a Afirka suka ci gaba da ɗaukaka gadon gidansu.

Aminu ya taso cikin ilimin addini da harkar kasuwanci. Ya fara karatu a makarantar allo kafin daga bisani ya shiga harkar kasuwanci.

Har zuwa lokacin da ya kai shekaru 17, ya ci gaba da harkokin kasuwanci da kai kaya zuwa wurare daban-daban a Arewacin Nijeriya.

A lokacin saboda babu manyan hanyoyi sosai, ya dogara da yin tafiye-tafiyens a raƙuma, jakuna da kekuna wajen kai kayayyaki.

Kodayake ya fito daga gidan arziƙi, Aminu ɗantata bai taɓa dogara da gadon gidansu ba.

Ya faɗaɗa kasuwancin da suka gada daga yin kasuwancin goro zuwa gina babbar daular kasuwanci da masana’antu a sassa daban-daban.

Kamfanoninsa sun taka rawa wajen gina muhimman cibiyoyin gwamnati irin su Nigerian Defence Academy a Kaduna da wasu gine-gine a Jami’ar Ahmadu Bello.

Ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fara saka hannun jari a harkar man fetur ta Nijeriya a kamfanin Eɗpress Petroleum & Gas Company.

A fannin harkar hada-hadar banki kuwa, ya taimaka wajen kafuwar bankin Jaiz Bank, bankin Musulunci na farko a Nijeriya.

Hakazalika, ya saka jari a noma da masana’antu, inda ya ci gaba da raya kasuwancin gyaɗa, auduga da masana’antar yadi.

A shekarar 1967, ya sayi jirginsa na farko, wanda hakan ya nuna bunƙasar kasuwancinsa.

Haka ma a shekarar 2009, ya mallaki jirgin sama na alfarma wanda darajarsa ta kai dala miliyan 38.

Harkokinsa sun wuce iyakokin Nijeriya. Ya mallaki kadarori a ƙasashen Saudiyya, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Masar, Birtaniya, Jamus da Amurka.

A wasu lokutan, ya kan ɗauki ‘ya’yansa zuwa aikin Hajji da Umrah da jirginsa na musamman, wanda ke nuni da yadda ya yi amfani da dukiyarsa wajen hidimar iyali da addini.
Shiga harkokin gwamnati da hidimta wa al’umma

Koda yake Dantata ya fi karkata zuwa ga harkokin kasuwanci, amma yana da sha’awar yi wa jama’a hidima, wanda hakan ya sa ya shiga siyasa.

A farkon shekarun 1960, an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai ƙarƙashin jam’iyyar Northern People’s Congress (NPC).

Daga baya ya zama Kwamishinan Tsare-tsare da Ci gaba a Jihar Kano ƙarƙashin Gwamnatin Audu Bako daga 1967 zuwa 1973.

Duk da irin warfin da yake da shi, bai nemi shahara ko matsayi ba.

Ya fi son kwatanta gaskiya da faɗin ra’ayinsa a bayyane, har ma yana ƙalubalantar shugabanni idan ya ga an kauce hanya.

A lokacin da girma ya kama shi, ya bayyana ra’ayinsa a fili cewa tsarin mulkin shugaban ƙasa na ci wa ƙasa kuɗi da yawa kuma baya bayar da sakamakon da ake buƙata.

Ya ce tsarin da Nijeriya ya dacewa ta koma shi ne tsarin majalisar dokoki, domin ya fi sauƙi da rinjaye wajen kula da kuɗi da jagoranci.
Alheri da ayyukan jin ƙai.

Abin da ya fi bayyana a rayuwar Aminu ɗantata shi ne alherinsa da sadaukarwarsa.

Koda yake ba ya bayyana ayyukansa a bainar jama’a, har ila yau ya canja rayuwar dubban mutane da hannunsa.

Ya gina makarantar sakandare ta mata a unguwar Dala da ke Jihar Kano, inda ya bayar da sama da Naira miliyan 50 don gina ɗakin karatu, banɗaki da rijiyar burtsatse da yawa.

Ya kafa Cibiyar Alhassan Dantata Haemodialysis Centre a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

A lokacin da ambaliyar ruwa ta auku a Maiduguri, ya bayar da tallafin Naira biliyan ɗaya da rabi.

Daga cikin labaran da suka fi taɓa zuciya dangane da shi, akwai na wani gida da aka yi rikici kan rabon gado, inda ya gina wa kowanen daga cikin waɗanda ke rigimar su bakwai gida, domin sulhun ta su.

Haka kuma ya ɗauki nauyin aikin hajji, gina masallatai, da kuma tallafa wa malamai da ɗalibai.

Gidansa da ke unguwar Koki a birnin Kano ya kasance mafaka ga talakawa, ’yan kasuwa da marasa galihu.

Duk da irin dukiyarsa, bai karɓi sarauta ko manyan muƙamai ba. Ya zauna cikin kamala da tawali’u, inda kowa ke girmama shi.
Jigo a wajen iyalansa da sauran jama’a

Aminu Dantata ya kasance shugaba a gida da waje. Ya auri mata da dama, kuma ya haifi yara wadanda sun manyanta.

Ya kasance mai ɗaukar nauyin tarbiyya da ilimin ‘ya’yansa — addini da na zamani. Ya kasance a tare da su a kasuwanci da harkokin yau da kullum.

Shekaru 12 na ƙarshen rayuwarsa ya mayar da hankali ne wajen iyalansa da karatu da kuma horar da matasa.

Koda ya kasance yana fama da rashin lafiya musamman wadda ta shafi girma, amma zuciyarsa cike take da natsuwa da lafiya.

A wata hirarsa ta ƙarshe, ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane ke banzatar da damar da Allah Ya ba su.

Ya ce: “Babu abin da ke burge ni a yanzu. Abin takaici ne yadda ba ma amfani da dama irin wadda Allah Ya ba mu.”

Ya ƙara da cewa: “Allah Ya hana yanke ƙauna,” alamar yadda imani ya tabbata a zuciyarsa har ƙarshen rayuwarsa.

A ranar 28 ga watan Yuni, 2025, Nijeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan ƙasar, Alhaji Aminu Alhassan Dantata bayan ya shafe shekaru 94 a duniya.

Ya rasu a birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wanda rasuwarsa ta kasance wani babban giɓi a tarihin ci gaban Nijeriya, musamman a fannin tattalin arziƙi da tallafa wa marasa ƙarfi.

Wannan rashi na ɗantata babban al’amari ne da ya shafi Nijeriya da ma Yammacin Afirka baki ɗaya.

Aminu ɗantata ya kasance mutum mai tasiri a fannonin kasuwanci, hidimar jama’a, addini da ayyukan jinƙai.

A wannan zamani da mutane da yawa ke rige-rigen nuna kai da nuna iko, shi ya kasance mutum na daban, mutum ne mai yawan yin shiru kuma mai cike da kamala da kuma sauƙin kai wajen mu’amala

By ukarofi