Likitoci sun tsunduma yajin aiki

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NARD) ta fara yajin aiki a wannan Laraba.

Shugaban ƙungiyar, Dr Emeka Orji, shi ne ya bayyana haka ga majiyarmu ranar Talata, inda ya ce likitoci za su tsunduma yajin aiki ranar Laraba, 26 ga Yuli, 2023 da misalin ƙarfe 12 na tsakar dare.

Orji ya ce, sun cim ma matsayar shiga yajin aikin ne a wajen taron shugabannin ƙungiyar da ya gudana cikin Yuli a Legas.

Ƙungiyar ta ce mabobinta sun shiga yajin aikin ne domin cim ma buƙatunsu a wajen gwamnati.

Ta ce buƙatun mambobin nata sun haɗa da neman a biya su kuɗin MRTF na 2023 da kuɗaɗen ariyas da suke bi bashi da sauransu.

Wannan na zuwa ne bayan da a baya ƙungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu a kan ta cim ma dukkan buƙatunta.

A wani yunƙuri na neman daƙile batun shiga yajin aikin, hakan ya sa Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya yi ganawar sirri da shugabannin NARD a ranar Litinin da ta gabata.

Bayan tattaunawar tasu, Abbas ya yi alƙawarin ganawa da Shugaba Bola Tinubu domin hana likitocin shuga yajin aikin tare da sanar da kafa wani kwamiti wanda zai yi zama da masu ruwa da tsaki don samar da maslaha.

Haka nan, Abbas ya roƙi ƙungiya da ta bai wa majalisar makonni biyu domin ba ta damar lalubo hanyar magance matsalar.

Sai dai, da alama ƙungiyar ba ta ji roƙon da Abbas ɗin ya yi ba inda tuni ta fara yajin aikin da ta ƙudiri aniya a wannan Laraba.