Luwaɗi da maɗigo a rumfar mulhidanci – Nazarin Ali Abubakar Sadiƙ

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ

A tarihin duniya, ba a taɓa samun guguwar wata aƙida da ta yaɗu cikin gaggawa irin ta ’yan luwaɗi da maɗigo ba (wadda ake wa laƙabi da LGBTƘ). Ba za a fahimci hakan ba sai an bibiyi tarihin wannan ƙungiya da ga kafuwarta zuwa yanzu a Amurka, wato Sodom (garin Annabi Ludu) na zamaninmu.

A ƙarni na 19 kaf da kuma farkon ƙarni na 20, yin luwaɗi a Amurka babban laifi ne da ke da hukuncin ɗauri. Kuma har zuwa shekarun 1950 akwai ƙungiyar ƙyamatar luwaɗi da ake wa laƙabi da McCarthyism, waɗanda ke farautar ’yan luwaɗi a jihohin Amurka. Amma a shekarun 1960-70 sai kotun ƙoli ta Amurka, saboda ƙarfin da ƙungiyar ’yan luwaɗi ta fara samu, su ka fara harbo doka ta farko wadda za ta ƙarfafa ’yancin yan luwaɗi ƙarƙashin gyaran doka ta 14 (14th Amendment), wadda ta ce “(hana) katsalandan ga ikon mutane su yi yadda su ka gama dama da jikinsu ko kutse cikin ma’amala ta mutane (namiji da namiji ko mace da mace), da kutsawa cikin ɗakunan kwanan mutane’.

Jihohi 18 su ka amince da dokar hana kallon luwaɗi da maɗigo a matsayin laifi, kodayake jihohi mafi yawa, musamman mabiya addinin Kirista da masu ra’ayin ’yan mazan jiya, sun yi watsi da dokar.

Amma har zuwa shekarar 1982, Jihar Georgia na da dokar luwaɗi, wadda ta ce “duk wanda aka samu da laifin luwaɗi, zai fuskanci hukuncin da bai gaza shekara guda a gidan kaso ba kuma wanda ba zai wuce shekaru 20 ba”.

Shari’ar Micheal Hardwick, wanda ’yan sanda ke nema bisa laifin maye, sun faɗa gidansa, inda su ka same shi yana luwaɗi. Bayan kotun ta ɗaure shi, sai ya ɗaukaka ƙara. Kotun Ɗaukaka Ƙara sai ta yi amfani da waccan doka ta kundi na 14, cewa ’yan sanda sun yi kutse cikin ɗakinsa, wanda ya karya ’yancinsa na ɗan adam. Ai kuwa wannan hukunci ya zama wani babban bango ga masu neman ’yancin ’yan luwaɗi.

Zuwa shekarar 1987, wato shekarar da ’yan LGBTQ su ka samar da Bible ɗinsu, wanda wasu ‘haziƙai masu fikira’, Marshall Kirk da Hunter Madsen, su ka wallafa, ya bai wa ’yan luwaɗi damar fara fantsama titinan Amurka da sigar neman ’yancinsu.

A wannan littafi nasu sun fito ƙarara su na cewa, “farfagandar da za su yi amfani da ita, za ta karkata wajen amfani da ilimi da basirar ɗan adam ta hanyar ilimi halayya (Psychology) da kimiyya da amfani da kafafen sadarwa.” Kuma wannan hanya ita suka fara a 1987, yadda a ƙasa da shekaru 40 sun sami ba kawai nasarar saka Kotun Ƙoli ta halasta auren jinsa ba, a’a har ma da ba su ikon zama masu tursasa wa maimakon waɗanda ake tursasawa, domin a Amurka duk wanda a yanzu zai muzguna wa ɗan luwaɗi ko maɗigo, zai sami kansa a kurkuku, ko rasa aiki ko rayuwarsa gabaɗaya.

Kwanan baya akwai wani mai gidan siyar da abinci da aka ɗaure a kurkuku, saboda kawai wasu ’yan daudu sun zo siya ya ce ba zai siyar musu ba. Su na kai shi ƙara kotu, a ka ɗaure shi. Mu na gani a Sweden an bayar da ikon a ƙona Ƙur’ani, amma ka na ƙyamatar ɗan luwaɗi, yanzu za ka tafi kurkuku.

A shekarar da suka wallafa waccan ƙasida tasu, 1987, Micheal Swift ya faɗa a wannan babban taro nasu cewa, “za mu koya wa ’ya’yanku luwaɗi, za mu bi su cikin makarantunsu, ɗakunan kwanansu, wuraren wasanni, har coci-coci da ƙungiyoyinsu na matasa.”… Ilai kuwa, cikin shekaru 30 sun cinye Amurka da yaƙi, ta zama ‘Sodom’ ɗin zamani, yadda su ka saka Kotun Ƙolin Amurka a aljihu da mamaye ’yan siyasa masu sassaucin ra’ayi (Liberal Democrats) irinsu Obama, yadda a lokacinsa aka yi dokar auren jinsi.

Abinda mutane ba su sani ba shine, wannan aƙida ta LGBTQ, ƙaramar ajanda ce ƙarƙashin babbar ajandar masu bauta wa shaiɗan (Satanism), domin a yaɗa mulhidanci (cewa babu Allah).

Sun fara ne da mamaye kimiyya da fasaha yadda a kullum ake karkata ta, domin nuna cewa babu Allah. Gane cewa kuma duk addinan duniya su na ƙyamatar luwaɗi, shi ya sa suka janyo su tare da ba su kariya. Sannan kuma babban yaƙinsu shine na rage yawan mutane, domin matuƙar addinai na haɓaka, buƙatarsu ta kore Allah cikin rayuwar mutane ba za ta samu ba. To, babu wani tsari da zai rage haihuwa a duniya kamar luwaɗi ko maɗigo.

Kar mu manta Allah ma Ya gaya ma na babban dalilin haramta luwaɗi tun a farko lokacin cikin surah da ayah na Ƙ29:29 “ashe lallai ku, ku na je wa maza, kuma ku na katse hanya?” Wato mutanen Luɗu, sakamakon yin luwaɗi ba su gane cewa, a wancan lokaci da babu mutane da yawa a doron ƙasa, ashe su na ƙoƙarin katse hanyar yaɗuwar mutane ba ne a doron ƙasa? (Akasarin tafsirai tun daga Tambari zuwa yanzu su na fassara katse hanya a wannan aya da yin fashi, alhali ba haka ake nufi ba). Shi ya sa yanzu ma ’yan bautar shaiɗan ke amfani da wannan hanya tare da kimiyya da ƙarfin siyasa da tattalin arziki wajen yaƙar Allah da addinai da ƙoƙarin rage yawan jama’a.

Sannu a hankali su na ta cin wannan yaƙin, domin su na amfani da zunzurutun ilimi ne. Misali, sun gano hanyar shirya yara su taso da rashin ƙyamatar luwaɗi ta hanyar gwajin yanayin ɗumin jikin jarirai a lokacin da aka haife su (body temperature). Akwai hanyoyi uku da ake gwajin; ta hammata (aɗillary), da ta baki (oral) da ta dubura (rectal). An saka masana su yi bincike su bayar da fatawar cewa, ta dubura ya fi inganci. Kuma a ƙasashen Yamma kusan duk jaririn da aka haifa ta haka ake auna ɗumin.

Illar ita ce, saka wa jaririn yatsa a dubura, ya na bashi sensation (wato jin taɓawa) ta farko bayan faɗo wa duniya, kuma dubura ita ce wajen da Allah ya ɗinke duk jijiyoyin jikin ɗan adam a wurin. Don haka wannan abu zai binne cikin ƙwaƙwalwar yaro mu’amalar luwaɗi, yadda idan ya girma ko ya ci karo da ita ba zai ƙyamace ta ba.

Sannan su na amfani da hikimar salancewa (desensitization) ta hanyar sauraro da kallo ta hanyar kambama labarin LGBTƘ da fina-finan batsa yadda yanzu an koya wa maza da mata, ko ba sa yin luwaɗi sai su riƙa sha’awar jima’i ta duburar mace.

A yanzu haka ƙasashen kusan 40 sun sahale wa auren jinsi, kuma Afirka ta Kudu, ita kaɗai ce a Afirka ta saka hannu. A lokacin Jonathan an hura wa Nijeriya wuta su saka hannu, amma Jonathan ya dage aka yi dokar watsi da hakan, wanda hakan na ɗaya daga dalilan da Amurka ta taya wajen kayar da shi a zaben 2015.

Sai yanzu aka yi zargin wai gwamnatin APC (ta Muslim-Muslim), idan rahoton jaridar Daily Trust ya zama gaskiya, cewa an saka hannu a daftarin Samoa, wanda aka shigar da maganar LGBTQ (daga baya an tabbatar da rahoton ba gaskiya ba ne har ma jaridar ta janye rahoton). Idan hakan ya tabbata, shugabanni sun ci amanarmu, dole a fito a yaƙi lamarin, domin yaƙi dai ba zai ƙare ba tsakanin rundunonin shaiɗan na sharri da rundunonin addinai da ake sa ran alheri.

Sai dai kash, rundunonin shaiɗan a yau, sun fi kuɗi, ilimin kimiyya da fasaha, kai har ma da basira, yayin da rundunonin addinai su ka rungumi jahilci da rarrabar kawuna. A yanzu kam rundunonin shaiɗan ludayinsu na kan dawo, kuma ba za mu iya juya teburin ba har sai ranar da mu ka dawo mu ka rungumi ilimi da aiki sau da ƙafa da halaye nagari da addinai su ka koya mana, ba zance a baki ba.

Ali Sadiƙ manazarcin al’amuran yau da kullum ne kuma mazaunin Kano.

By ukarofi