Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani ma’aikacin lafiya a ƙaramar Hukumar Giwa, Malam Ibrahim Sunusi Sarki wanda kuma shi ne Magajin garin Ruguji, ya bayyana cewa ma’aikatan lafiya a matakin farko da malaman makarantun firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi suna ɗanɗana kuɗarsu sakamakon rashin biyansu albashin watan Fabrairu da Maris.
Ibrahim Sunusi ya ce da dama daga cikin ma’aikatan da abin ya shafa na fama da ɗawainiyar iyali wajen samar musu da abinci, musamman a cikin watan Ramadan ɗin nan, inda ya bayyana cewa wannan matsala ta jefa su cikin mawuyacin hali.
Saboda haka a madadinsa yake kira ga mahukunta da su gaggauta ɗaukar matakin rage musu raɗaɗin wahalar da suke fuskanta.
“Jihar Kaduna ta kasance jagaba wajen tara kuɗaɗen shiga (IGR) a tsakanin jihohin Arewa 19 a cikin shekaru biyu da suka gabata, sakamakon gyare-gyaren haraji da Gwamna Uba Sani ya aiwatar.
“Saboda wannan ci gaba, muna kira ga Malam Uba Sani da ya bai wa dukkan ƙananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna cikakken ‘yanci wajen tafiyar da al’amuransu. Wannan zai ba su damar biyan albashin ma’aikata cikin lokaci, tare da inganta ayyukan kiwon lafiya, ilimi, da sauran muhimman ayyuka a matakin ƙananan hukumomi,” inji Ibrahim.
Ibrahim Sunusi ya ƙara da cewa gaggauta magance wannan matsala ta biyan kowane ma’aikaci haƙƙinsa zai kawo sauƙi ga ma’aikatan da abin ya shafa, tare da bunƙasa ingancin ayyuka a matakin ƙasa bakiɗaya.
Sai dai a wani bincike da Manhaja ta yi, ta gano cewa gwamnatin Jihar Kaduna a yanzu haka tana cigaba da biyan wasu ma’aikatan lafiya da na ƙananan hukumomi albashinsu da su ke bi a ƙarshen watan nan da muke ciki.
