Ma’aikatan CBN da suka ajiye aiki sun maka bankin a kotu

  Sun buƙaci diyyar Naira biliyan 30

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata dambarwa ta ɓarke tsakanin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da tsofaffin ma’aikatansa da aka sallama daga aiki a shekarar 2024.

Tsofaffin ma’aikatan sun yi iƙirarin cewa babban bankin ya karya dokokinsa da kansa da dokokin da suka shafi ƙwadago a Nijeriya da dokokin ɗaukar aiki.

Tsofaffin ma’aikatan dai sun samu wakilcin Stephen Gana da wasu 32, inda masu ƙarar suka shigar da ƙara a gaban kotun ma’aikata ta Nijeriya (NICN) a Abuja.

A cikin takardun shigar da ƙarar, an bayyana matakin da CBN ya ɗauka – cikin wata takarda da ke nuna sake fasalin ma’aikata ta bankin ta ranar 5 ga watan Afirilun 2024 – ya saɓa wa sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Nijeriya da da dokokin ma’aikata na babban bankin (HRPPM).

Masu ƙarar sun ce babu tuntuɓa ko adalci na sauraronsu da aka nuna kamar yadda doka ta tanada.

A cikin abubuwan da kotun za ta duba da ke ƙunshe cikin dokokin Ma’aikata ta 2017, akwai batun batun jin koken ma’aikatan kafin da bayan sallamar su da babban bankin ya yi.

Sannan masu ƙarar sun ce sam amfani da batun sake fasalin ma’aikata a matsayin dalilin sallamarsu abu ne da ya saɓa wa doka.

Ma’aikatan da aka dakatar na neman kotu ta ayyana watsi da sallamarsu da bankin ya yi da tabbatar da su a matsayin ma’aikata.

Sannan sun buƙaci kotun ta tilasta wa bankin dawo da su bakin aiki da biyansu albashinsu da duk wani ‘yan kun-ji-kun-ji daga lokacin da aka sallame su kawo lokacin da za su dawo bakin aiki da kuma yi wa bankin gargaɗin ɗaukar makamancin wannan mataki nan gaba ba tare da bin ƙa’ida ba.

Dokar HRPPM, kamar yadda sashe na 16.4.1 ya ƙunsa, ya buƙaci a yi tattaunawar haɗin guiwa da majalisar gudanarwar bankin da bin ƙa’ida kafin ɗaukar matakin da bankin ya ɗauka

Sannan ma’aikatan da aka sallama na neman diyyar Naira biliyan 30 kan sanya su cikin damuwa da mawuyacin hali da taɓa muhibbarsu sakamakon sallamarsu da aka yi.

Haka kuma sun buƙaci a biya su Naira miliyan 500 na kuɗin da suka kashe wajen shigar da ƙara domin neman haƙƙinsu.

Kotun a ranar 20 ga watan Nuwabar2024 ta buƙaci a samu masala a tsakanin ɓangarorin biyu.

A cikin wasu takardu da premium ta samu ganin su kan shari’ar da mai shari’a Justice O. A. Obaseki Osaghae ta yi, ta lura cewa Stephen Salawu Gana ne ya wakilci ma’aikatan da aka sallama inda kuma babban lauya mai darajar SAN Inam Wilson ya wakilci bankin CBN.

A yayin da mai shari’ar Obaseki Osaghae, ta buƙaci da su je su yi sulhu kamar yadda sashe na 20 na kundin kotun kare haƙƙin ma’aikata (NICA) ta shekarar 2006 ya ƙunsa.

“A ra’ayina ina ganin ya kamata ɓangarorin biyu su fara ƙoƙarin samun masalaha kan wannan matsala,” ta faɗa.

An dai ɗage sauraron shari’ar har zuwa ranar 29 ga watan Janairun 2025 domin jin kowanne ɓangare da cigaban da aka samu game da batun neman masalaha a tsakaninsu.

Rahotanni sun nuna cewa babban bankin ya gudanar da tsabtare ma’aikatansa ne ta fuskoki guda 4 tsakanin watannin Maris da Mayun 2024 wanda ya jefa ma’aikatan cikin mawuyacin halin rashin kuɗi.

Wasu daga cikin ma’aikatan sun ce an biya su kuɗin diyya da bai kai 5,000 inda wasu suka ce an riƙe musu garatutinsu a matsayin biyan bashin rancen da suka karɓa.

An dai alaƙanta korar ma’aikatan ne da sake fasalin ma’aikata da ayyukan bankin, sai dai korarrun ma’aikatan bankin sun ƙalubalanci wannan mataki da cewa ya saɓa wa dokar bankin CBN domin akwai buƙatar samun amincewar majalisar gudanarwar bankin kafin ɗaukar irin wannan mataki kan ma’aikata.

Wani daga cikin ma’aikatan da aka sallama ya ce, “ba wata shaida da ta nuna an samu sahalewar majalisar gudanarwar bankin kafin sallamar, bankin ya ɗauki wannan mataki ne a ƙashin kansa ba tare da bin ƙa’ida ba. Wannan ce ta sa tilas mu nemi haƙƙinmu a kotu.”

Izuwa yanzu dai rahotanni sun nuna cewa ma’aikata 218 ne wannan mataki ya shafa wanda ya afku a watannin Maris da Mayun 2024.

Kuma an sallami ma’aikatan ne kashi-kashi har 4 a ranar 15 da 22 ga watan Maris, sai 24 ga watan Mayun 2024.

Kaso na farko su ne wannan mataki ya fi duka domin ba inda aka bayyana ƙarara a takardar kan cewa za a ba su diyya ko akasin haka.

Sai dai sauran ma’aikatan da aka sallama a ranar 22 ga watan Maris da 24 ga watan Mayu da 5 ga watan Afirilu, bankin ya yi alƙawarin cewa zai lissafa haƙƙinsu tare da turo musu daga baya duk da babu cikakken bayani kan nau’in diyyar da za a ba su na sallama ko takamaimai lokacin da za su samu haƙƙin nasu.

Ga ma’aikatan da suka ɗauki shekaru 10 zuwa 20 suna aiki, an ba su kuɗin diyyar Naira 5,000 zuwa 6,000.

Wannan ya biyo bayan dokar bankin na amfani da garatutin ma’aikaci wajen warware wani bashi da bankin ke binsa da sauran kowanne irin nau’in bashi.

Sai dai Babban Bankin ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne daidai da dokar ɗaukar su aiki.

Sannan banki ya yi da’awar biyan ma’aikatan dukkan haƙƙoƙinsu na watanni uku daga lokacin da ya ba su notis kamar yadda yake ƙunshe cikin yarjejeniyar sallama idan hakan ba shi da alaƙa da aikata wani laifi ko karya ƙa’idar aiki.

CBN ya bayyana sallamar ma’aikatan a matsayin wani mataki na sake fasalin ayyukan bankin wanda yake da ikon yin hakan bisa doka tare da ƙaryata zargin da ma’aikatan da aka sallama suka yi na cewa bankin bai yi musu adalci ba kuma ya saɓa ƙa’ida.

Sai dai Manhaja ta kira mai magana da yawun CBN, Hakama Ali, amma wayarsa ba ta shiga kuma bai ba da amsar saƙon kar ta kwana ba kan gaskiyar rashin kyakkyawar sallama ga ma’aikatan da aka kora. Haka ma saƙon imel da aka aika masa, bai ba da amsa ba har zuwa lokacin da muka tuntuɓe shi.