Ma’aurata su zama masu biyayya da girmama juna – Bello ɓutu-ɓutu

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Dan majalisar dokoki mai wakiltar ƙananan hukumomin Rimin Gado da Tofa, mataimakin shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano, Hon. Muhmmmad Bello Butubutu ya yi kira ga ma’aurata musamman sabbin aure  ango da amarya su zama masu biyayya da girmama juna,  “domin shi aure ibada ne sunnar Annabi, mata su bi mazajensu sau da ƙafa akan kowane umurni da bai saɓawa shari’a ba.”

Ya bayyana haka ne da yake jawabi  jim kaɗan bayan ɗaurin auren ‘ya’yansa da aka yi  a masallacin Rijiyar Zaki a makon jiya. 

Ya ce  da babba da yaro da jami’an gwamnati da wakilan Gwamnan Kano da mataimakinsa da ‘yan majalisu na jihar Kano da waɗanda suka zo daga ciki da wajen Kano da wanda suka yi fatan alkhairi daga nesa ya ji daɗi ya yi farin ciki da yi wa Allah godiya bisa wannan karamci da aka nuna masa.

Hon. Muhammad Bello Butubutu ya ce a matsayinsu na ɗan siyasa kullum tarbiyya da suke yi wa ‘yan siyasa irin wanda suka gada ne, ta yin biyayya da haƙuri, gaskiya da riƙon amana da yin aiki tuƙuru a duk matsayi da mutum ya samu kan sa.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin na jihar Kano ya gode wa al’ummar mazaɓar da yake wakilta na Rimin Gado da Tofa a  majalisar Kano bisa irin goyon baya da suke ba shi a kowane lokaci kuma ci gada da ta ya shi addu’a yanda zai cigaba da jajircewa wajen sauke nauyin wakilci da suka ɗora masa.

By ukarofi