
Daga BELLO A. BABAJI
Mazauna birane da ƙauyuka da ke gefen kogin Benue a Jihar Taraba sun fara ƙaura da nome ababen da suka shuka bayan ruwa ya fara haɗiye gonaki sakamakon buɗe madatsar Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru.
Bincike ya nuna cewa adadin ruwa da ke kogin Benue ya ƙaru da wani kaso wanda hakan ya sa gonakin da ke kusa suka dilmiye a ruwa.
Wani matuƙin jirgin ruwa mai suna Jalo Ibbi, ya bayyana wa jaridar ‘Daily Trust’ cewa ruwa ya fara ƙaruwa ne sa’o’i 20 da suka gabata wanda hakan ya sabbaba al’umma suka shiga tsaka-mai-wuya ganin yadda gonakinsu suka fara haɗiɗiyewa.
Ya ce,
0 tuni mutane a garuruwan Amar da Kambari na ƙaramar hukumar Karim-Lamido suka fara ƙaura daga gidajensu zuwa wasu wuraren inda wasu kuma ke cigaba da zama.
Ya kuma ce, kawo yanzu ba a san matakin ɓarnar da ruwan ya yi ba tun tsawon sati biyu da hukumomi a Kamaru suka sako wani sashi na Lagdo.
