Kwamitin gidauniyar rabon tallafi ga mabuƙata na Bafarawa ya fara aiki a Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An ƙaddamar da kwamitin da zai tattara bayanan buƙatun mutanen da gidauniyar Dakta Attahiru Bafarawa, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, za ta taimaka wa da kayan tallafi a faɗin jihar.

Shugaban Hukumar kula da Zakka da Waƙafi ta Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki ke jagorantar kwamitin tare da wasu mambobin da aka zaɓo daga ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar da mambobin babban kwamitin.

Tsohon Gwamnan na Sakkwato, wanda kuma shi ne garkuwar Sakkwato, ya bayyana dalilan da suka sa zai bayar da gudunmawar da ta kai Naira biliyan ɗaya don rage raɗaɗin talauci da jama’a da dama ke fama da shi.

Bafarawa ya bayyana haka ne a wurin ƙaddamar da gidauniyar da za ta raba kuɗin ga mabuƙata a wani gagarumin taro da ya gudana a gidansa da ke birnin Sakkwato.

Ya ce, wannan wata hanya ce da ya ke so ya yi amfani da ita wajen sakantawa al’ummar Sakkwato game da alheri da ƙaunar da suka nuna masa a lokacin da ya ke riƙe da madafun iko a jihar, tare da alƙawarin cigaba hidimta musu har iyakar rayuwarsa.

“A shekarun da na shafe a matsayin gwamna, na yi ƙoƙari wajen ganin jama’ar Jihar Sakkwato sun samu damar cin gajiyar demokraɗiyya ƙarƙashin gwamnatina wajen gabatar da ayyukan raya ƙasa musamman a ɓangarorin shimfiɗa hanyoyi da inganta harkokin kiwon lafiya, da raya ilmi. Hakan ya sa na tabbatar da an yi amfani da dukiyar Sakkwatawa yanda ya kamata.”

“Idan na tuna irin soyayyar da Sakkwatawa suka nuna min sai na so na wuce abin da na yi a yanzu, la’akari da yadda aka tafiyar da gwamnati. Abu ne sananne ana iya samun kuskure wajen tafiyar da shugabanci, don haka irin waɗannan ayyuka na jinƙai da tallafawa al’umma suke da muhimmanci wajen kawo sauyi da samun rabo a wurin Allah. Wannan shi ne abin da ya ƙara min azama don rama alherin da Sakkwatawa suka yi min ba tare da la’akari da duk wani alheri da na yi a lokacin da nake gwamna ba.”

“Shekaru 17 bayan na sauka a gwamna, ina murna da farincikin ganin al’umma ba ta sauya ba. Zamana ɗan shekara 70, da haihuwa burina ya cika duk wani giɓi da aka samu a dangantaka ta da al’umma”, inji Bafarawa.

Garkuwar Sakkwato ya kuma buƙaci Kwamitin da aka ɗora wa alhakin gudanar da wannan aiki, da ya yi aiki tsakani da Allah.

By Babaji