A ranar Juma’a ne kwamitin da ke kula da gyare-gyare a kan albashin ma’aikatan gwamnati ya gana a ranar dangane da sabon samfurin mafi ƙarancin albashi kuma sun amince cewa za a sanya ranar aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a ranar 29 ga Yuli, 2024.
Wannan dai na zuwa ne a wata takardar fahimtar juna da aka fitar a ƙarshen taron wanda wakilinmu ya gani a Abuja ranar Juma’a.
Kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa a biya tallafin ƙari ga ma’aikata na 35,000 wanda gwamnati ta dakatar har zuwa ranar 28 ga Yuli, 2024.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Didi Walson-Jack ya lura cewa gwamnati ta lura da yanayin tattalin arzikin ƙasar kafin ta ɗauki matakin.
“Kwamitin ya gudanar da tarurruka huɗu kuma ya yi la’akari da duk bayanan da Gwamnatin Tarayya da ɓangaren Ƙungiyar Ƙwadago suka gabatar. Ta kuma yi la’akari da yanayin tattalin arziki da ikon Gwamnatin Tarayya na biya da kuma ɗorewar duk wani gyara na albashin da ya taso daga aiwatar da dokar mafi karancin albashi na ƙasa ta 2024.
Takardar fahimtar junan ta ci gaba da ba da shawarar cewa hukumar NSIWC za ta samar da samfuran albashin da suka dace ga sauran tsarin albashi domim aiwatarwa.
“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan da suka dace don rage raɗaɗin da ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ke fama da su a sakamakon ƙaruwar farashin mai da aka yi a baya-bayan nan.
Sai dai da yake mayar da martani a wata hira da ƴan jarida, shugaban yaɗa labarai na ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Benson Upah, ya caccaki matakin da gwamnati ta ɗauka, yana mai bayyana hakan a matsayin wanda ba za a amince da shi ba.
Har ila yau, mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, Timmy Etim, ya soki matakin da gwamnati ta ɗauka.
Ya ce tun da ƙaramin ministan ƙwadago, Nkiruka Onyejeocha, ya shaidawa ma’aikata a watan Mayu cewa sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki a watan Mayu, bai dace gwamnati ta yi watsi da alƙawarin ba.
“ Ƙaramin ministan Ƙwadago, a lokacin bikin ranar Mayu, ya ce biyan sabon mafi ƙarancin albashi na kasa zai fara aiki daga ranar 1 ga Mayu.
A halin da ake ciki, wasu ma’aikatan gwamnati sun koka da jinkirin fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
