Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce akwai buƙatar Gwamnatin Nijeriya ta sake duba yiwuwar ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikatan ƙasar, domin a cewarta, naira 70,000 ya yi kaɗan a yanzu da tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare.
A watan Yulin bara ne dai shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu a sabuwar dokar ƙara mafi ƙarancin albashi, inda ya ƙara ƙaramin albashi na ma’aikatan ƙasar daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, duk da cewa wasu jihohin na biyan sama da haka.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito ƙungiyar na cewa hauhawar farashin kayayyakin buƙata a ƙasar ne ya sa mafi ƙarancin albashin naira 70,000 ba ya isar ma’aikacin ƙasar gudanar da abubuwan da suke buƙata na rayuwar yau da kullum, kamar yadda muƙaddashin babban sakataren NLC, Mr Benson Upah ya shaida wa NAN a ranar Lahadi a Abuja.
“Maganar gaskiya naira 70,000 ya yi kaɗan a wannan yanayin na taɓarɓarewar arziki a Nijeriya. Ma’aikata na fuskantar ƙalubale sosai, kuma idan gwamnati ba ta ɗauki matakin da ya dace ba, lallai ma’aikatan ƙasar za su shiga cikin damuwa sosai.
“Tuni mun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya game da wannnan matsalar, kuma muna fata za ta yi abin da ya dace duba da irin yadda tattalin arzikin ƙasar yake ciki.”
Ya bayyana matakin a matsayin abin maraba da kuma farkawa.
Shugaban ASCSN ya bayyana cewa matakan da ƙananan hukumomi suka ɗauka ya zama ishara ga gwamnatin tarayya.
“Tun da farko, a lokacin tattaunawar, buƙatarmu ita ce a biya mu albashi, kuma mun gabatar da N250,000 a matsayin ma’auni mai ma’ana.
“Mun gaya wa gwamnati cewa duk abin da ya gaza hakan sai ya kai ma’aikaci zuwa kofar ofis, ba ya koma gida,” inji shi.
Ya bayyana cewa, sakamakon hauhawar farashin wutar lantarki, sufuri, da kuma farashin kayan abinci, N70,000 ya yi hasarar sa.
Ya ƙara da cewa “Mu kasance masu gaskiya, ko da kun biya kudin wutar lantarki daga cikin N70,000, abin da ya rage ba zai iya ci gaba da riƙe iyali har tsawon kwanaki 10.”
Mohammed ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da karin ma’aikata tare da manyan tsare-tsare don rage tsadar rayuwa da suka hada da gidaje masu saukin kuɗi, kiwon lafiya, da tallafin sufuri.
ɓangaren ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka zanta da NAN sun kuma bayyana damuwarsu kan taɓarɓarewar tattalin arziki, inda suka ce rayuwa ta kara yin wahala a halin da ake ciki.
