Daga ABUBAKAR MUHAMMAD TAHEER
Magajin Rafin Haɗejia, Alhaji Muhammad Babandede Sarkiki ya rasu a daren Lahadin da ta gabata a ƙasar Misra bayan shafe tsawo lokaci yana fama da jinya.
Marigayin shi ne Mahaifin Tsohon Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa CG. Muhammad Babandede.
A halin rayuwarsa, alumma ta amfana da marigayin ta fannoni da da dama, kuma ya kasance uba ga al’ummar ƙasar Haɗejia da ma jihar Jigawa baki ɗaya.
Zuwa yanzu Masaurautar Haɗejia ba ta sanar da lokacin jana’izar sa ba har sai an kawo gawarsa daga ƙasar Misra.
