Shari’ar Gwamnan Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jinkirtar da yanke hukunci zuwa gaba

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta Abuja ta jinkirtar da yanke hukunci kan ƙarar da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya shigar zuwa wani lokaci da ba ta bayyana ba.

Abba ya ɗaukaka ƙara ne inda yake ƙalubalantar hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe wadda ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe gwamnan zaɓen jihar Kano.

Idan za a iya tunawa, Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe a jihar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Oluyemi Akintan Osadebay, ta soke nasarar da Abba ya samu a zaɓen bayan da ta zabtare ƙuri’u 165,663 daga cikin adadin ƙuri’un da ya samu.

Bayan kammala zaɓen ne INEC ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gudana ran 18 ga Maris, 2023, bayan da ta ce ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Gawuna ya rufa masa baya da ƙuri’u 890,705.

Daga bisani APC ta garzaya Kutun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen, inda ta yi zargin an tafka arzigizon ƙuri’u a zaɓen.

Bayan binciken da ta yi, Kotun ta amince da ƙorafin APC inda ta ce an gano takardun ƙuri’u sama da 160,000 waɗanda INEC ba ta sanya wa hannu ba daga ƙuri’un da Abba ya samu.

Bayan ɗebe ƙuri’un da aka gano babu sa hannun INEC, hakan ya sa Yusuf ya tsira da ƙuri’u 853,939 yayin da Ganuwa ya tashi da ƙuri’u 890,705.

Wannan ya sa Abba ya garzaya Kotun Ɗaukaka Kara don kare nasararsa inda aka ci gaba da tafka shari’a.

Sai dai bayan kammala sauraren duka ɓangarorin da shari’ar ta shafa a ranar Litinin, Kotun ta bayyana cewa, “An jinkirtar da bayyana hukuncin shari’ar zuwa wani lokaci wanda da za a sanar da ɓangarorin da shari’ar ta shafa.”