A kwanakin baya ne alqalin kotun da ke shari’ar laifukan fyaɗe da cin zarafin cikin gida da ke Ikeja, ya yanke wa daraktan kula da lafiya na gidauniyar kula da cutar daji, Dokta Olufemi Olaleye, hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan laifin yi wa ’yar uwar matarsa fyaɗe.
An tuhumi Olaleye da laifuka biyu na lalata da kuma keta haddin ’yar uwar matarsa, laifukan da ake zarginsa da aikata tsakanin Maris 2020 da Nuwamba 2021.
An gurfanar da wanda ake tuhuma a ranar 30 ga Nuwamba, 2022 kuma ya musanta aikata laifin.
Kwana ɗaya da faruwar, kotun da ke zamanta a Legas, ta yanke wa wani mutum mai suna Joseph Ekanem hukuncin ɗaurin rai-da-rai a gidan yari bisa laifin lalata ’yar makwabcinsa ’yar shekara 13.
Da yake yanke hukuncin, alƙalin kotun, Mai shari’a Abiola Soladoye, ya bayyana cewa Ekanem yana da laifuka biyu da ake tuhumarsa da su na cin zarafi ta hanyar keta haddi, saɓanin sashe na 137 da 261 na dokokin laifuka na Jihar Legas, 2015.
A wani shari’ar da ake cigaba da yi, wani mataimakin Sufeton ’yan sanda, Babatunde Ashifat, ya bayyana wa kotun laifukan lalata da cin zarafin gida da ke Ikeja yadda wani mutum mai suna Jelili Lawal ya yi wa wata tsohuwa ’yar shekara 80 fyaɗe har lahira.
A watan Satumban bana, rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen jihar Legas, ta bayyana cewa ta samu rahoton aikata laifukan fyaɗe 111 tsakanin Afrilu zuwa Yuni 2023.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin, ya ce rundunar ta damu da yadda ake samun ƙaruwar cin zarafi a jihar.
Ya ce, a cikin wannan lokaci an samu laifukan fyaɗe guda 14 da kuma laifuka 56 na rikicin cikin gida, sannan an gurfanar da waɗanda ake zargi 99 a gaban kotu a cikin wa’adin.
Ya kuma ƙara da cewa, a halin yanzu ana gudanar da bincike kan ƙararraki 83, wanda hakan ke nuna ƙudurin hukumar na gurfanar da duk wani rikici na cikin gida da na jinsi a jihar Legas.
Rahotanni sun nuna cewa an samu ƙaruwar laifukan fyaɗe a faɗin ƙasar. Wannan lamari mai takaici ne da ke haifar da fargaba da damuwa a tsakanin al’ummar ƙasar inda da dama suka buƙaci jami’an tsaro da su ƙara zage damtse wajen ganin an shawo kan matsalar.
A Gombe, rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta samu rahoton aikata laifukan fyaɗe aƙalla 43 tsakanin watan Janairu zuwa Yulin 2023.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Oqua Etim, wanda ya ce laifin babban ƙalubale ne a jihar, ya kuma bayyana cewa an gurfanar da 37 daga cikin ƙararrakin da aka gabatar gaban kotu yayin ake cigaba da binciken shida.
Abin damun a cikin wannan lamari shi ne waɗanda abin ya shafa sun haɗa da yara ƙanana yayin da a wasu lokuta, masu aikata laifin ’yan uwa ne yaran ne.
Etim ya ƙara da cewa, yayin da ake cigaba da kame masu laifin da a ƙarshe aka gurfanar da su a gaban kotu, ana cigaba da bayar da shawarwarin haɗin gwiwa don duba yadda ake samun ƙaruwar cin zarafin mata a jihar.
A kwanakin baya ne dai rahotanni suka ce an yi wa wasu ɗalibai mata huɗu fyaɗe a jami’ar Tai Solarin University of Education (TASUED) da ke Ijagun da ke Ijebu-Ode a jihar Ogun a lokacin da wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne suka kutsa kai cikin ɗakin kwanan ɗalibai a makarantar.
A matsayinmu na jarida mai son faɗin gaskiya da tsare adalci mun damu matuqa game da barazanar fyaɗe a Nijeriya, kuma mun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a ɗauki matakan gaggawa don dakatar da lamarin.
Abin takaici ne a ganinmu, cewa a cikin ’yan watannin da suka gabata an samu rahotannin aikata laifukan fyaɗe da dama a faɗin ƙasar, yayin da wasu da dama ba a kai rahotonsu ba saboda wasu dalilai masu alaƙa da nuna ƙyama da kuma zargi.
An ce ga duk wani ƙara ɗaya da aka kai, shida ba a kai rahoton su ba sakamakon abubuwa daban-daban, da suka haɗa da nuna ƙyama, rashin sanin yadda za a samu tallafi da dai sauransu.
Sai dai jihohin Katsina da Kano da Taraba da Zamfara duk sauran jihohin da babban birnin tarayya Abuja sun amince da dokar hana cin zarafin jama’a (VAPP) da aka kafa a shekarar 2015.
Tsarin shari’a a Nijeriya kan laifukan da suka shafi laifuffuka su ne: Dokar Criminal Code Act (‘Criminal Code’) wacce ta shafi jihohin Kudu, Penal Code wanda ya shafi jihohin Arewa, Dokar Hana Cin Zarafin Jama’a ta 2015 (VAPP), da sauran dokoki.
Bambance-bambancen da ke tsakanin ƙa’idojin laifuka da dokokin hukunta laifuka na yanki ne kuma su na nuna bambance-bambancen al’adu da addini.
A qarqashin dokar cin zarafi ga mutane ta 2015, mafi ƙarancin hukuncin fyaɗe shi ne zaman gidan yari na shekaru 12 ba tare da tara ba kuma mafi girman hukuncin shi ne ɗaurin rai da rai.
Dokar VAPP tana aiki ne a babban birnin tarayya Abuja da Legas da Ekiti da kuma wasu jihohin Nijeriya waɗanda ko dai sun amince da shi ko kuma sun kawo irin waɗannan dokoki da suka haɗa da jihohin Anambra da Ebonyi da Oyo.
A cikin rahotonta na shekarar 2021, Amnesty International a Nijeriya, ta ce fyaɗe na cigaba da kasancewa ɗaya daga cikin laifukan take haƙƙin ɗan Adam da ya zama ruwan dare a Nijeriya.
Ta ce duk da ayyana dokar ta-vaci da hukumomin Nijeriya suka yi kan cin zarafin mata, fyaɗe yana cigaba da faruwa a matakan tashin hankali inda aka qi yin adalci ga mafi yawan waɗanda ke aikata laifin, masu fyaɗe su na gujewa hukunci, da kuma ɗaruruwan laifukan fyaɗe da ba a bayar da rahotonsu ba saboda cin hanci da rashawa.
Ganin haka ne a kwanakin baya alƙalin babbar kotun jihar Ribas Eberechi Wike ta bayar da shawarar yin dandaƙa ga mutanen da aka samu da laifin lalata ƙananan yara.
Ta dage cewa hukuncin da ake yi a halin yanzu bai cika tsauri ba, ta ƙara da cewa matakin zai hana masu lalata ƙananan yara cigaba da aikata laifin.
A ra’ayin Blueprint Manhaja, ya kamata a ɗauki ƙwararan matakai don magance matsalar fyaɗe a Nijeriya tare ba bai wa batun muhimmancin da ya dace.
Dole ne ƙasar ta kare mata da ‘yan mata ta hanyar tabbatar da cewa masu aikata laifukan fyaɗe sun fuskanci shari’a kuma waɗanda abinya shafa sun sami kariya da taimakon jin daɗi daga gwamnati.
Akwai buqatar bayar da shawarwari da wayar da kan waɗanda abin ya shafa su yi magana koyaushe lokacin da aka zalunce.
Bai kamata riqa a rufe shari’o’in fyaɗe ba, sai dai a fallasa su domin a gurfanar da masu laifi yadda ya kamata domin amfanin waɗanda abin ya shafa, da al’umma da kuma zama a matsayin darasi.
