Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE,
Magoya bayan Hon. Zakariyya Jidda, ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye ƙarƙashin jam’iyyar APC, sun yi watsi da zarge-zargen cewa ana shirin yin maguɗi a tsarin sake tantance membobin jam’iyyar ta hanyar aiki da na’urar lantarki da kuma zaɓen fidda gwani a jihar Gombe.
Ƙungiyar magoya bayan, ƙarƙashin jagorancin shugabanta Abubakar Saleh, ta bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe, balle makama da yaudara da kuma na siyasa, tana mai jaddada cewa Hon. Jidda da magoya bayansa suna goyon bayan sahihin tsari mai cike da gaskiya da adalci kamar yadda APC ta ƙasa ta tanada.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, da safiyar Asabar magoya bayan sun ce dole ne aikin sake tantance membobin jam’iyyar ya gudana bisa tsarin da jam’iyyar APC ta ƙasa ta amince da shi, inda suka ce takardun rajista na lantarki da tsarin ya samar kaɗai ya kamata a amince da su.
Sanarwar ta ƙara da cewa amfani da katunan zama memba da ba su cikin tsarin da aka amince da shi ko kuma saka wasu sharuɗɗa daban na iya kawo cikas ga sahihancin aikin tare da buɗe ƙofa ga magudi.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga shugabannin APC a jihar Gombe da su tabbatar da adalci, gaskiya da kuma bai wa dukkan mambobin jam’iyyar da suka yi rajista dama iri ɗaya yayin gudanar da aikin.
“Abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne ƙarfafa APC da bunƙasa haɗin kai a cikin jam’iyyar, maimakon yaɗa zarge-zargen da za su iya haddasa rarrabuwar kai da rashin yarda tsakanin mambobi,” in ji sanarwar.
Magoya bayan sun kuma roƙi dukkan masu ruwa da tsaki da su bari aikin sake tantance membobin ya gudana cikin lumana tare da bin umarnin shugabancin APC na ƙasa.
