Mahaifina ke yin nasara a gasar nuna amfanin gona duk shekara a Katsina – Aminu Rayyanu

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wani babban manomi a Jihar Katsina mai suna Alhaji Aminu Rayyanu ɗandume, Sarkin noman Jihar Katsina dake ƙaramar Hukumar ɗandume, ya bayyana cewar tun daga shekaru aru-aru baya da suka gabata a kowace shekara idan gwamnatin jihar Katsina ta gudanar da taron wasan nuna amfanin gona mahaifinsa ne yake samun nasarar lashe gasar gabaɗaya.

Alhaji Aminu Rayyanu ɗandume, Sarkin noman Jihar katsina ya yi wannan tsokaci ne a Katsina a lokacin da yake nuna farin cikinsa dangane da samun nasarar lashe gasar ta nuna amfanin gonar a wannan shekarar ta bana, inda bayan kammala taron gasar kwamishina mai kukawa  da ma’aikatar aikin gona na jihar Katsina, Farfesa Ahmed Mahamud Bakori ya sake jadda wa Alhaji Aminu Rayyanu ɗandume rawanin sarautarsu ta Sarkin noman Jihar Katsina, sannan Jaridar Blueprint Manhaja ta keɓe shi waje ɗaya domin jin ta bakinsa dangane da wannan al’amari.

Sarkin noman na Jihar Katsina ya cigaba da warware zare da abawa dangane da al’amuran da jiɓanci harkokin noman abinci, inda Aminu Rayyanu ɗandume ya cigaba da cewa tun yana yaro ɗan ƙarami ya taso ne ya ga gidansu ana noma, ya ce yana ɗan ƙaramin yaron mahaifinsa ya cigaba da koya masa yadda ake gudanar da harkokin noma tare da dabarun yin noman baki ɗaya, har ga shi Allah Ubangiji ya bashi ikon sanin komai har ma yana koyawa waɗansu yadda ake yin noman gabaɗaya.

Ya cigaba da cewa noman kayan abinci  yana da matukar muhimmanci a ƙasa bisa ga hakan ne ya ce duk da yasan irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ta Katsina take yi a wajen bunƙasa harkokin noman a binci a duk faɗin jihar baki ɗaya yake son ya ƙara ba ta shawarwari ta yadda za ta ƙara hobbasa a wajen tallafawa ɓangaran gudanar da harkokin noman abinci da sauran makamantansu.

Ya ƙara da cewa ya sani cewar a kowacce shekara gwamnatin jihar Katsina tana bayar da tallafin takin zamani ga ƙananan manoma, to ya kamata ta ƙirƙiro wani tsari wanda suma manyan manoman ya zama cewar suna samun irin wannan tallafi na takin zamani domin ƙara masu ƙwarin guiwa ta wannan ɓangaren domin su noma abincin da zai wadaci jihar Katsina dama ƙasar nan.

Haka nan kuma ya cigaba da jinjinawa gwamnatin ta jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin hazikin gwamnan jihar Dakta Alhaji Dikko Umar Raɗɗa a ƙoƙarinsa na faɗaɗa harkokin tsaro a duk faɗin jihar, ya ce al’ummar jihar Katsina suna godiya dangane da wannan al’amari. 

By ukarofi