Mahara sun kashe Janar Ahmed a Abuja

Daga UMAR M. GOMBE

Wasu mahara sun kashe Manjo Janar Hassan Ahmed, tsohon Provost Marshal na Sojojin Najeriya a Abuja.

An kashe Ahmed ne jiya Alhamis da daddare a yankin Abaji na Abuja.

Maharan sun kuma sace ‘yar uwar marigayin mai suna Safina Ahmed, wadda suka kuskure a matsayin matarsa.

Wata majiya ta kusa da marigayin ta bayyana cewa, marigayin suna kan hanyarsu ta dawowa daga Okene ne inda maharan suka far musu.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta ne inda nan take Ahmed ya rasu, shi kuwa direban motar sai ya yi likimo kamar ya mutu saboda raunin da ya ji, don haka sai suka yi gaba da Safina.

Bayanai sun nuna Janar Ahmed ba shi da wasu dakarun rakiya yayin tafiyar tasa wanda hakan ya sanya maharan suka samu kai wa gare shi.

Sanarwar da Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na Sojojin Nijeriya, Brigadier General Onyema Nwacjukwu ya fitar, ta nuna an kai gawar marigayin an adana ta a Asibitin Ƙungiyar Matan Sojoji da ke Abuja.

Kazalika, sanarwar ta ce a wannan Juma’ar za a yi jana’izar matigayin a maƙabartar Lungi Barracks da misalin ƙarfe goma na safe.

Rundunar ta ce Shugaban Sojoji, Faruk Yahaya da ma ilahirin sojojin Nijeriya sun nuna alhininsu dangane da wannan rashi.

A kwanan nan ne Shugaban Sojoji, Faruk Yahaya, ya naɗa marigayin a matsayin Darakta a babban ofishin sojoji da ke Abuja.