Nijeriya na neman addu’ar kowa!

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Mafi yawan talakawan Nijeriya sun yi tsammanin cewa, kawo yanzu ’yan ƙasar sun fita daga cikin halin ƙuncin da suka tsinci kansu a ƙarƙashin gwamnatocin baya, to amma har yanzu al’amura sun ƙi miƙewa, su tafi yadda ya kamata, duk da cewa, an zaɓo shugaban da ake da kyakkyawan zato a kansa, sannan kuma har kawo yanzu ba a taɓa zargin sa da aikata almundahana ko muna-muna da rashawa ba.

To, amma duk da haka, baya ga tsananin halin talauci, fatara da ƙuncin rayuwa da talaka a Nijeriya ke fama da su, a yanzu dai kullum sababbin masifu ne ke cigaba da dabaibaye rayuwarsa. Tattalin arziki, siyasa, tsaro, shugabanci, ilimi, tarbiyya, lafiya; duka komai ya lalace ya kai gargara a cikin Nijeriya. An kai gargarar da ta ke da wuya ka iya ɗaga wani fanni guda ɗaya yanzu a ƙasar da za ka ɗaga ka ce ‘wannan kam sambarka’.

A tattalin arziki, kowa ya san yadda rashin aikin yi ya yi katutu. Masu aikin yi ma, musamman waɗanda ke da sana’ar hannu, a halin yanzu da ƙyar su ke samun abinda su ke kai wa bakin salati. Mutum za ka gani kullum sai ya fita sana’a, amma kuskuren rashin fita na rana ɗaya kacal sai ya haifar ma sa da cin bashi ko kuma azumin dole a cikin gidansa.

Mazauna gidaje haya, da ƙyar su ke iya biya a ƙarshen kowacce shekara, da ƙyar mafi yawan iyaye su ke iya biya wa yaransu kuɗin makaranta; ga shi kuma makarantun gwamnati ba su da nagarta ko ƙanƙanuwa, haka nan mafi yawan iyaye da ƙyar su ke iya yi wa ’ya’yansu nata kayan ɗaki, idan aurensu ya zo, su ma samari da ƙyar su ke haɗa kayan lefe, domin yanzu iyayen samari ba su iya yi mu su aure, kamar yadda a shekarun da ake yi lokacin auren fari, musamman a ƙasar Hausa.

Al’amuran siyasa sun ta’azzara ƙwarai da gaske. Aminci a tsakanin ’yan siyasa ya yi matuƙar rauni. A yanzu duk yadda ku ka kai da kusaci ko aminci tsakaninka da wani ɗan siyasa, abu ne mai sauƙi a wayi gari ya bar ka kacokam, saboda kawai abin duniyar da zai samu a wani wajen. Duk yadda mai goyon bayanka ya kai da koɗa ka, duk yadda mai goyon bayanka ya kai ga fito wa bainar jama’a ya na kare ka, ya kuma na zuga ka, ba zai jin kunya gobe ko jibi ya dawo ya zage ka ba, matuƙar wani ya fi ka farashi a wajensa, kuma komai daɗewarku a tare.

An kai munzalin da kowa mafita ya ke nemar wa kansa, ba al’umma gabaɗaya ba, an kai munzalin da za a iya haɗa baki da kowa a cutar da kai, don biyan buƙatar siyasa kurum. Su ma jam’iyyu su na ganin ta kansu, domin za su taƙarƙare su tsayar da ɗan takara a ƙarƙashin tutarsu, amma katsam sai a wayi gari ya fice daga cikin jam’iyyar tasa ba tare da yi ma sa wani ƙwaƙƙwaran laifi ba.

A batun tsaro kuwa sai dai a ce, ‘inna lillahi wa inna ilaihir raji’un’ kurum! Ka na gida a ɗakinka cikin fargaba ka ke, a tafe a kan hanya cikin fargaba ka ke, a wajen aikinka cikin fargaba ka ke, a makaranta cikin fargaba ka ke, a filin wasa cikin fargaba ka ke. Da rana fargaba, da daddare fargaba. Lokacin sanyi ko damina ko bazara kowa a fargaba ya ke. Ka na farin kaya a cikin fargaba ka ke, haka nan ka na mai kayan sarki a cikin fargaba ka ke.

A kullum kuma a koyaushe kashe rayuka kawai a ke yi babu ji babu gani.
Shugabanni sun zama mutanen banza, marasa cika alƙawari, masu kare muradunsu kawai ba na ƙasa ko al’umma ba. Talakawa sun zama mutanen kawai! Kowa ya mallaki ’yan ku]insa burinsa shi ne ya tsaya takara ya mulki jama’a, domin kawai shi ma ya shiga jerin waɗanda ke sace dukiyar jama’ar ƙasa. Masu riƙe da madafun iko sun daina sauraron masu yi mu su wa’azi; kunnuwansu sun zama na sauraron masu zuga su na tunzura su, su na kai mu su tsurku da gulmar mutane. Annamimanci dai kaɗahan! Shugabannin sun koma aikin kare kujerunsa, ba kare ƙasa ba. Da yawan malamai sun zama makwaɗaita. Irin waɗannan malaman su na yin wa’azi ne kawai gwargwadon abin da zai ƙara mu su nauyin aljihu!

Sha’anin ilimi ya taɓarɓare ya kai gargara. Babu wata makartar firamare ko sakandare da ke iya samar da yaran da za su iya yin magana da minti biyar da harshen Turanci. Tuni an wuce wannan babin. Yanzu neman takardar shaida kawai a ke yi, ba ainihin madarar ilimin ba. Waɗanda haƙƙin kula da sha’anin ilimi ke hannunsu sun fi damuwa da gine-gine fiye da ingancin ilimin. Kullum a ka gudanar da bincike sai sakamakon ya nuna cewa, ci-baya a ke yi, ba cigaba ba. Miliyoyin yara su na ta faman gararamba a titina, ba su zuwa makaranta.

Tarbiyyar al’umma ta riga ta shiga wani mawuyacin hali. Ha’inci da almundahana sun kama zukatanmu. Zinace-zinace da luwaɗi da maɗigo da tsafe-tsafe da shirka sun zama ruwan dare. Musulmi da yawa ba su damu da yin sallah a cikin jam’i ba, Kirista da dama ba su damu da zuwa coci a ranakun Lahadi ba. A na neman aure a cikin saɓon Allah ta hanyar abin da a ka ƙago na ‘Shan Minti’, kowa burinsa shi ne ya mallaki kuɗin taƙama da alfahari.

Sha’anin lafiya ya zama bin tausayi. Asibitocin gwamnati sun zama tamkar maƙabartu. Ba a samun wata cikakkiyar kulawa daga masu ruwa da tsaki a sha’anin lafiya. Gwamnati ta fi damuwa da yin gine-gine fiye da sanya kayan aiki a asibitocin. Kuɗin magani da na tiyata sun fi ƙarfin talakan Nijeriya, ballantana kuma ɗaukar nauyin jinyarsa zuwa ƙasashen waje. A yanzu ɗan Nijeriya idan har ya na so ya sami waraka, to tilas sai ya fita ƙasar waje neman magani. Ka ga talaka ya shiga uku kenan!

Shin yaya a ke so ’yan Nijeriya su yi ne wai? Haƙiƙa Nijeriya sai du’a’i! Babbar mafita ita ce, gyaran hali da kuma samar da shugabanni nagari, waɗanda za a dauwama cikin yi u su addu’o’in samun nagarta, kyakkyawar zuciya da aiki tuƙuru. Faƙat!!!