Bello ga ma’aikatansa: Ku rungumi noman shinkafa don kyautata rayuwarku

Daga BASHIR ISAH

An yi kira ga ma’aikatan gwamnati na jihar Neja da su rungumi hanyoyin da za su taimaka musu wajen samun kuɗaɗen shiga fiye da albashin da suke samu domin samun madogara bayan sun yi murabus daga aiki.

Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello, shi ne ya yi wannan kira a wajen bikin ƙaddamar da Ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya (RIFAN) da aka gudanar ran Alhamis a Minna, babban birnin jihar don amfanin ma’aikatan gwamnatin jihar a wannan damina.

Bello ya ce ƙaddamar da shirin cikar wani ɓangare ne na ƙudurin da yake fa shi kan ma’aikatan gwamnati na neman inganta rayuwarsu domin samun abin dogaro musamman ma bayan sun yi ritaya daga aiki ta yadda su ma wasu za su amfana da su.

Gwaman ya buƙaci kada wani ma’aikaci ya bari a baro shi baya dangane da shirin saboda irin amfanin da ya ce shirin ke tattare da shi wanda zai buɗa wa rayuwarsu hanyoyin samu da dama.

Ya ce burinsa shi ne ya ga ma’aikatan jihar su ma sun zama masu ɗaukar ma’aikata a ƙarƙashinsu albarakcin shirin.

Ya ci gaba da cewa, sama da ma’aikata 4000 ake sa ran su amfana da shirin a rukunin farko, tare da cewa zai tattauna da Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin ƙara adadin waɗanda za su amfana da shirin a rukuni na gaba.

Baya ga alwashin da Bello ya sha na mara wa duk wani shiri da zai amfani ma’aikatansa baya, haka nan ya umarci Shugabar Ma’aikatan Jihar, Hajiya Salamatu Abubakar, da ta ƙirƙiro sabbin hanyoyin da ma’aikatan jihar za su amfana da su.

A nata ɓangaren, Hajiya Salamatu Abubakar ta ce, an ƙaddamar da wannan shiri ne domin tallafawa wajen wadata ƙasa da abinci da kuma ƙarin hanyar samun kuɗin shiga ga ma’aikata.

Ta ƙara da cewa, tuni dubban ma’aikata tsakanin ƙananan hukumomi da jiha suka nuna sha’awarsu na shiga shirin, kuma ma har an yi nisa da shirin ɗaukar bayanansu.

Da yake jawabi a wajen taron, kodinetan RIFAN na jihar Neja, Alh. Idris Usman Makaranta, ya ce ana sa ran manoma 42, 000 su noma filin gona kadada 66,000, tare da cewa gwamnatin jihar ta tanadi injunan sarrafa shinkafa guda 100,000.

RIFAN tare da haɗin gwiwar ofishin shugaban ma’aikatan jihar ne suka shirya shirin ƙarƙashin shirin nan na bai wa manoma rance na CBN, wato ‘Anchor Borrowers Scheme’.