Mahawara ta tashi bayan Apostle Suleman ya shawarci samari su daina taimakon ’yan mata

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban limamin coci Apostle Johnson Suleman, wanda kuma shi ne mu’assasin Omega Fire Ministries Worldwide, ya haifar da muhawara ta yanar gizo bayan da ya buƙaci samari da su mayar da hankali wajen tallafa wa ‘yan uwansu maza maimakon mata.

Limamin cocin ya bayyana haka ne a yayin wani wa’azi na baya-bayan nan da ya bazu a shafukan sada zumunta.

Da yake bayyana ra’ayinsa, Suleman ya bayyana cewa, daga ƙwarewarsa, mazan da suke ɗaukaka wasu mazaje sun fi samun ci gaban rayuwa.

Ya yarda cewa duk wasu matan na da kirki da nuna godiya, amma taimaka musu a wasu lokuta kan haifar da ruɗani.

Yayin da yake jawabi, ya ce: “A matsayinka na saurayi, bari na ba ka shawara; ka taimaki maza fiye da mata: ‘Aah papa, kana adawa da mata?’ A’a, bari mata su taimaki kansu. Ka san dalilin da ya sa? Idan ka taimaki namiji, ka samu ƙungiya ne.

“Lokacin da kuka taimaki mace, ku jira abin kunya. Ba duka ba, amma za su kai kashi goma… A lukuta da dama gara ka tainaki namiji.

Duk da sanin cewa kalaman nasa na iya kawo cece-kuce, Suleman ya jaddada cewa saƙon nasa ya ta’allaƙa ne kan ra’ayinsa.

“Na san wannan magana ba za ta yi wa wasu daɗi ba amma ban damu ba, ina magana ne daga ƙwarewata. Wannan ra’ayi ne kuma na cancanci na faɗi,” inji shi.

By ukarofi