Mai shari’a Dije Aboki ta yaba wa Shugabar FIDA

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Babbar Mai Shara’a ta Jihar Kano, Hon Dije Aboki ta yaba wa shugabar Ƙungiyar Mata Lƙuyoyi ta Ƙasa, reshan Jihar Kano Baristar Hajiya Bilkisu Ibrahim Sulaiman, dangane da yadda ta ke ƙoƙari wajen tabbatar da samun haƙƙin marasa galihu da kuma ƙoƙarin bunƙasa ilimin mata lauyoyi da sauran al’amura na ciyar da al’umma.

Ta ce,  a wannan lokaci na shugabancin Hajiya Bilkisu Ibrahim Sulaiman, shugabar ƙungiyar mata lauyoyi da ake kira FIDA babbar mai shara’a ta Jihar Kano Hon Dije Aboki, ta bayana haka ne a lokacin da ayyarin lauyoyi mata ƙarƙashin shugabancin shugaban FIDA ta ƙasa reshen jihar Kano Hajiya Bilkisu Ibrahim, ta jagoranci ayarin yan ƙungiyar ta lauyoyi mata domun neman haɗin kai ga babban mai shara’ƙ ta Kano wajen ayyuka da kuma ƙoƙarin da ƙungiyar FIDA ta ke yi domun cigaban al’ummar Kano da ƙasa bakiɗaya.

Ita ma a jawabinta shugabar FIDA Bilkisu Ibrahim, ta ce gamsuwa da yadda mace ta farko da ta samu wannan muƙami kuma ta ke tafiyar da shi yadda yakamata wannan abin a yaba wa babban mai shara’a ne ta Jihar Kano Hon Dije Aboki, kuma wajibi ne wannan ƙungiya dama ɗaukacin lauyoyi da sauran al’umma su ba ta haɗin kai da yin adu’a wajen samun nasarar aikinta nasarar mata lauyoyi ne nasarar mata alƙalai ne nasarar lauyoyi ne nasarar al’ummar Kano ne nasarar gwamnati ne dama ƙasa bakiɗaya kamar dai yadda Hajiya Bilkisu Ibrahim Sulaiman, ta bayana a lokacin wannan ziyara da ayarin ƙungiyar lauyoyi mata FIDA ta ƙasa reshen Jihar Kano suka ziyarci babbar mai shari’a Hon Dije Aboki.

By ukarofi