Mai yiwuwa NLC ta dakatar da shirinta na shiga yajin aiki

Da alama ƙungiyoyin jwadago na NLC da TUC ba za su shiga yajin aikin da suka yi wa shirya domin ba da zarafin ci gaba da tattauna game da batun aiwatar da yarjejeniyon da suka cimma da ɓangaren gwamnati.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwa bayan taron da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Lahadi.

Da yammacin Lahadin da ta gabata Gwamnatin Tarayya ta yi zama na musamman da jagororin ƙungiyoyin ƙwadago domin tattauna mafita dangane da yajin aikin da ƙungiyoyin suka ƙuduri aniya.

Yayin zaman, gwamnati ta amince a kan za ta gaggauta samar da motocin safa masu amfani da gas don rage wahalhalun zirga-zirgar da cire tallafin mai ya haifar.

Kazalika, gwamnati ta ce za ta fara biyan N25,000 duk wata ga magidanta miliyan 15 na tsawon wata uku daga watan Oktoba zuwa Disamba, 2023.

Taron ya samu halartar gwamnoni da ministoci.