Majalisa na son mayar da zaɓen Shugaban ƙasa a Nuwamba 2026

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar dattawa da ta wakilai suna ba da shawarar cewa a gudanar da zaɓukan ‘yan majalisar wakilai da na gwamnoni a watan Nuwambar 2026, saɓanin watan Fabrairu ko Maris na shekarar zaɓe.

Shawarar tana ƙunshe ne a cikin daftarin gyare-gyare ga dokar zaɓe ta 2022, wanda aka tattauna a ranar Litinin yayin wani taron jin ra’ayin jama’a na kwana daya da kwamitin hadin gwiwa kan al’amuran zabe, wanda Sanata Simon Lalong (APC, Filato ta Kudu) ya jagoranta.

A cewar sashe na 4 (7) na gyaran da aka gabatar, “Za a gudanar da zabukan ofishin shugaban ƙasa da na gwamnan jihar nan da kwanaki 185 kafin cikar wa’adin ofishin shugaban ƙasa na ƙarshe.”

Yayin da wa’adin mulkin gwamnati ya kare a ranar 29 ga Mayu, 2027, hakan na nufin za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni ne a wajajen watan Nuwamba na 2026, domin kwanaki 185 kafin ranar 29 ga Mayu ya kasance a cikin wannan watan.

Hakazalika, shawarar zaɓen ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a ƙarƙashin sashe na 4(5) ya ce za a gudanar da irin wannan zaɓe ne nan da kwanaki 185 kafin ranar da kowace majalisar ta tsaya.

‘Yan majalisar dai sun ce kwaskwarimar na da nufin ba da isasshen lokaci don warware takaddamar zaɓe kafin a rantsar da waɗanda suka yi nasara.

Da yake karin haske, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, Hon. Adebayo Balogun, ya ce gyaran zai taimaka wajen hana faruwar al’amuran da ke faruwa a kotu bayan waɗanda suka yi nasara sun karɓi ragamar mulki.

“Muna ba da shawarar cewa a kammala dukkan shari’ar zaben kafin a rantsar da wadanda suka lashe zaɓen,” inji Balogun.

“Don cimma wannan, muna ba da shawarar cewa a rage kwanakin 180 na yanzu da aka ba da izinin yanke hukuncin kotun zuwa kwanaki 90, yayin da yanke hukunci da Kotun Koli ya kamata kowane ya ɗauki fiye da kwanaki 60 – duk a cikin kwanaki 185 kafin rantsar da su.”

Ya kara da cewa shawarar zata kuma bukaci gyara daidai sashi na 285 da na 139 na kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 (kamar yadda aka gyara) domin daidaitawa da sabon tsarin lokaci.

A wurin taron jama’a, masu ruwa da tsaki da dama – ciki har da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da Farfesa Abdullahi Zuru ya wakilta – sun goyi bayan yunƙurin yin amfani da na’urar zaɓe da watsa sakamakon na’urar don inganta gaskiya.

A ƙarƙashin sashe na 60(5) na gyaran da aka gabatar, dokar za ta sanya wajabta wa shugabannin jami’an watsa sakamako ta hanyar lantarki da kuma da hannu. Rashin yin hakan zai jawo hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari, ko tarar Naira miliyan 1, ko kuma duka biyun.

Canje-canjen da aka tsara ya kuma gabatar da jefa ƙuri’a da wuri, wanda ke ba da damar wasu nau’ikan ‘yan Nijeriya – kamar jami’an tsaro, jami’an INEC, da kwararrun ‘yan jarida, masu sa ido, da ma’aikatan wucin gadi – su kada kuri’a har kwanaki 14 kafin ranar zaɓe.

Takardar kwamitin haɗin gwiwa ta kuma ba da shawarar cire lokutan zaɓe daga kundin tsarin mulki da shigar da su cikin dokar zaɓe, don yin gyare-gyare a nan gaba.

“Sashe na 28, wanda yanzu aka koma matsayin sashe na 27 (5-7), an gabatar da shi ne don nuna wannan sauyi da kuma buɗe takunkumin da kundin tsarin mulki ya tanada akan lokutan zaɓe,” inji takardar.

Masu ruwa da tsaki a zaman taron sun amince da sauye-sauyen, inda suka bayyana su a matsayin matakan da suka dace don inganta sahihancin zaɓen Nijeriya, da ƙarfafa kwarjinin hukumomi, da tabbatar da cewa shari’o’in da suka biyo bayan zaɓukan ba su ci karo da sabbin wa’adi ba.

By ukarofi