Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Malalisar Dattawa ta amince wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ciyo basin Dala biliyan shida domin rage bashin da ake bin Nijeriya da kuma gyaran tashoshin jiragen ruwa da ke Jihar Legas.
Wannan rance zai ƙara yawan bashin da ake bin Nijeriya daga dala biliyan 110.3 zuwa Dala biliyan 115.3.
Sauran amfanin da za a yi da kuɗaɗen sun haɗa da ayyukan gine-gine, da kuma cike gibin da aka samu a kasafin kuɗin ƙasar.
A ranar Talata Majalisar ta amince da buƙatar ƙasar bayan karanta wasiƙu biyu daban-daban da Shugaban ƙasa ya aika kan batun.
A cikin wata wasika da ya aika wa Shugaban Majalisar dattawa, Godswill Akpabio, Shugaban ƙasa ya nemi rancen dala biliyan 5 daga bankin First Abu Dhabi Bank da ke ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Shugaban ƙasa ya roƙi majalisar da ta ba da “amincewa cikin gaggawa,” inda ya bayyana cewa za a yi amfani da takardun kuɗin Naira a matsayin jingina.
A wata wasika daban, Shugaban ya nemi rancen Dala biliyan 1 domin gyaran Tashar Jiragen Ruwa ta Legas da ta Tin Can Island.
Ya ce rancen zai fito ne daga Citibank London tare da tallafin UK Eɗport Finance (UKEF), domin sabunta tashoshin jiragen ruwa da ke Jihar Legas da nufin inganta tsaro, aiki da kuma ingancinsu.
Shugaban ƙasa ya bayyana cewa aikin gyaran zai magance matsalolin da suka daɗe suna damun tashoshin, ya ƙara tsaro da bin ƙa’idojin duniya, tare da tallafa wa ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Ya ƙara da cewa rancen zai kasance da wa’adin biyan bashin shekaru 14, ciki har da karin wa’adin watanni 48 na samun damar amfani da kuɗin.
Haka kuma akwai kuɗin “aɓailability fee” na kashi 1.1% da kuma “UKEF premium” na kashi 1.07%.
Tun da farko, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rancen ƙasashen waje da na cikin gida, Sanata Aliyu Magatarkada Wamakko, ya bayyana cewa kwamitin ya yi nazari sosai kan bukatar rancen kafin ya gabatar da rahotonsa a gaban majalisa domin amincewa.
