Majalisar Dattawa ta amince da kasafin 2026 ba tare da bincike kan ƙarin buƙatar Tinubu ba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2026 a ranar Talata, bayan ƙara Naira tiriliyan 9.3 da Bola Tinubu ya nema, wanda ya kai jimillar kasafin zuwa N68.323 tiriliyan.

Baya ga amincewa da buƙatar shugaban ƙasar, majalisar ta ƙara Naira biliyan 623 a kan adadin da aka gabatar, inda aka ɗaga kasafin daga N67.7 tiriliyan zuwa N68.323 tiriliyan.

An amince da kasafin ne ta hanyar jefa ƙuri’a ta murya (ɓoice ɓote), inda yawancin sanatoci suka nuna goyon bayansu.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da amincewar kasafin bayan kammala ƙuri’ar.

Sanatoci sun amince da kasafin ne bayan nazartar rahoton da shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Dattawa, Adeola Olamilekan, ya gabatar.

A cikin rahoton, ya ba da shawarar ware:

N4.799 tiriliyan don canja wurin doka (statutory transfers) da N15.809 tiriliyan don biyan bashi da kuma N16.427 tiriliyan don kashe-kashen yau da kullum (ba na bashi ba). Sai kuma wata  N32.287 tiriliyan don ayyukan ci gaba (capital eɗpenditure).

Rahotanni sun nuna cewa amincewar kasafin ta zo ne ’yan awanni bayan shugaban majalisar ya karanta wasiƙar Shugaban ƙasa da ke neman a ƙara kasafin da N9.3 tiriliyan, daga N58.47 tiriliyan zuwa N67.7 tiriliyan.

A cikin wasiƙar, Tinubu ya bayyana cewa ƙarin kuɗin zai taimaka wajen kammala manyan ayyukan raya ƙasa da aka gada daga kasafin baya.

Ya kuma ce za a yi amfani da kuɗin wajen tallafa wa manyan ayyukan sufuri da kuma tabbatar da daidaiton tattalin arziki, tare da rage matsin lamba a kasuwar kuɗi ta cikin gida.

Sai dai yayin tattaunawa kan kasafin, sanatoci ba su yi tambayoyi ko cikakken bincike kan buƙatar ƙarin kuɗin da shugaban ƙasa ya gabatar ba, lamarin da ya ja hankali a fagen siyasa da tattalin arziki.

By ukarofi