Daga USMAN KAROFI
Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojojin Nijeriya. Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya aike da wasiƙar neman amincewa da nadinsa ga majalisar dokoki ta Ƙasa, bayan ya naɗa shi a matsayin muƙaddashi sakamakon rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Tabbatar da naɗin ya biyo bayan amincewar da aka samu a ranar Alhamis, lokacin da najalisar ta ɗauki shawarar kwamitin riƙon ƙwarya da ya gudanar da tantancewar sa.
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar, Hon. Babajimi Benson, wanda ya jagoranci tantancewar, ya bayyana cewa kwamitin ya gamsu da ƙwarewar Janar Oluyede da tarihin aikinsa.
A cewar Benson, an gudanar da tantancewar ne a ranar Laraba, inda aka nazarci takardun shaidarsa kuma aka tambaye shi kan muhimman batutuwa. Ya bayyana cewa Janar Oluyede ya yi bayanin da ya gamsar da kwamitin, yana mai cewa, “Muna ba da shawarar cewa Majalisar ta amince da tabbacin naɗinsa.”
Kwamitin ya ƙara da cewa wanda aka naɗa ya nuna zurfin ilimi da kwarewa a fagen ayyukan soja. Bayan haka, mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ya kira mambobin don kaɗa ƙuri’ar murya kan naɗin, kuma dukkan su sun amince da shi ba tare da saɓani ba.
