Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙulla yarjejeniya da sojojin Nijeriya don magance matsalolin tsaro

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙulla yarjejeniya da rundunar sojin ƙasar Najeriya domin magance matsalolin tsaro a faɗin ƙasar haɗa da yankin sahel.

Babban Wakilin Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Africa ta Tsakiya, Mai girma Mahamat Khatir Annadif, shi ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar sa ga Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya a Shelkwatar rundunar da ke Abuja. Inda yaba wa rundunar sojin Nijeriya kan sha’anin magance matsalolin tsaro ƙasar da kuma yankin sahel.

Jakadan ya na tare ne da Wakilin Musamman na Babban Sakataren Majalisar, Mai girma Mr Francois Luncemy Fall wanda ya ƙarfafa amfani da dabarun yaƙi wajen magance tashin hankali a ƙasar da kuma yankin sahel.

Ya bayyana cewa duk rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasashen Africa sanadiyar yaƙin Libiya ne. Daga nan, ya yi alƙawarin haɗa kai da Najeriya wajen magance kwararar ƙananan makamai da gano masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda.

A jawabin sa, Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya bayyana cewa dakarun tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro na samin nasarar kawo ƙarshen ta’addanci a Najeriya.

Babban hafsan ya kuma buƙaci haɗin gwiwa domin taimakon waɗanda ta’adanci ya shafa, gano masu tallafa wa ta’addancin, magance shige da ficen makamai da gudunmawar fasaha.