Sojoji sun hallaka maharin ‘yan awaren Biafra

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Dakarun da ke gudanar da Atisayen GOLDEN DAWN sun sami nasarar hallaka wani mahari ɗan ƙungiyar ‘yan awaren Biafra bayan ya kai hari a sansanin rundunar da ke Amaekpu da ke ƙaramar hukumar Ohafia a jihar Abia ranar Alhamis da ta gabata.

Rundunar ta bayyana wannan nasarar da ta samu ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar ran Alhamis mai ɗauke da sa hannun Birgediya Janar Onyema Nwachukwu wanda shi ne daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojojin Nigeriya.

A cewar rundunar, “Maharan waɗanda ke ɗauke da makamai a cikin motoci sun buɗe wuta kan sansanin dakarun, inda suka fuskanci turjiya aka kuma murƙushe ɗaya daga cikin su. Bayan sauran Maharan sun tsere, dakarun sun ƙwato bindiga ƙirar harbi ka ruga.

“Bayan ‘yan ta’addan sun tsere a sakamakon shan kashi ne, dakarun sansanin Ohaozara da ke jihar Ebonyi suka cafke su a Eda, inda suka ƙwace motoci uku da kame mahari ɗaya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *