Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi alla-wadai da kisan mutane a Borno da neman hukunta masu hannu ciki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta yi tir da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula a yankin Kukawa na Jihar Borno dake Arewa maso Gabashin Nijeriya.

A wata sanarwa da Kodinetan Jin-ƙai na Majalisar a Nijeriya, Mohamed Malick ya fitar, MƊD ta bayyana kisan mutane 40 da wasu haramtattun mayaƙa suka yi a garin Dumba a ranar 12 ga watan Junairu a matsayin abin tashin hankali.

Mayaƙan sun kashe mutanen ne waɗanda galibin su manoma da masunta ne bayan zargin su da taka dokarsu ta hana gudanar da harkokin gona a yankin.

Malick ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda suka samu raunuka tare da fatan su samu waraka cikin lokaci, ya na mai cewa MƊD tana tare da su da gwamnatin jihar.

Ya kuma buƙaci da a gano waɗanda suka gudanar da kisan tare da gurfanar da su don su fuskanci hukuncin doka, kamar yadda dokokin ƙasa da na Ƙasa-da-ƙasa game da ƴancin ɗan-adam suka tanada.

Ya ƙara da cewa, harin da wasu ƴan ta’adda da dama suka kai a shekarar 2024 sun sake jefa al’ummomin Jihohin Borno, Yobe da Adamawa cikin ɗar-ɗar.

Kazalika, ya yi kira da a ƙara ƙarfafa matakan tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda dokar Jin-ƙai ta Ƙasa-da-ƙasa da ta buƙaci a tsare fararen hula daga cutarwa.

By ukarofi