
Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON).
Hakan ya biyo bayan rahoton kwamitin harkokin waje na majalisar dattawa, wanda Sanata Abubakar Sani Bello (APC, Niger North) ke jagoranta, bayan sun yi masa tantancewa.
A zaman majalisar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya jagoranta, majalisar ta kuma amince da naɗin Alhaji Saidu Usman Dakingari a matsayin jakadan Najeriya wanda ba ma’aikacin diflomasiyya na dindindin ba (Non-Career Ambassador).
Kazalika, majalisar ta tabbatar da naɗin Rear Admiral Jamila Abubakar Sadiq (mai ritaya) a matsayin Kwamishinan Zaɓe na ƙasa a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), mai wakiltar yankin Arewa maso Gabas.
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa akan harkokin zaɓe, Sanata Simon Bako Lalong, ya ce an yi cikakken bincike da tantancewa kafin amincewa da sabon kwamishinan na INEC.
