Ramadana: Gwamnan Sokoto ya amince da biyan albashin Maris gabanin Ƙaramar Sallah

Spread the love

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da fara biyan albashin watan Maris tun daga ranar Juma’a 13 ga watan Maris, domin bai wa ma’aikatan gwamnati damar gudanar da shagulgulan Sallah cikin sauƙi.

‎Sanarwar ta fito ne ta bakin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Bawa.

‎A cewar sanarwar, biyan albashin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnatin jiha, ma’aikatan ƙananan hukumomi, da kuma masu karɓar fansho a faɗin jihar.
‎Gwamna Ahmed Aliyu, wanda a halin yanzu yake ƙasar Saudi Arabia domin gudanar da ibadar Umrah, ya buƙaci ma’aikatan gwamnati su cigaba da nuna ƙwazo, gaskiya da jajircewa wajen sauke nauyin ayyukansu.

‎Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa ta tabbatar da biyan albashi akan lokaci, tare da cigaba da biyan basussukan kuɗaɗen fansho da aka gada.

Kazalika, ya tunatar da cewa gwamnatinsa ta ɗauki sabbin ma’aikata kimanin dubu uku domin ƙarfafa ayyukan ma’aikatun gwamnati da kuma rage matsalar rashin aikin yi a jihar.

By Babaji