CBN ya umarci bankuna su saka takunkumi ga masu asusun da suka saɓa sharuɗɗan karɓar bashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna su hana bayar da sabon bashi ga kwastomomin da rancensu ya zama wanda aka gaza musamman manyan masu bashi.

Sanarwar da Daraktan Kula da Bankuna, Olubukola Akinwunmi ya sanya wa hannu ta ce duk wanda aka saka sunansa a tsarin Credit Risk Management System (CRMS) ko bayanan cibiyoyin bashi, to ba zai samu sabon lamuni ba.

Haka kuma, za a sanya masa takunkumi na wasu ayyukan banki da za su bayar da damar samun wani ƙarin bashi.

Babban bankin ya kuma ce matakin ya shafi manyan masu bashi da suka wuce ƙa’idar ‘Single Obligor Limit’ domin kare bankuna da tsarin kuɗin ƙasa daga haɗarin basussuka.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da bankin da haɗin-gwiwar sauran cibiyoyin kuɗaɗe ke ƙoƙarin shawo kan matsalolin fuskantar barazanar karyewa a sanadiyyar yawan basussukan da aka gaza biya.

By Babaji