Majalisar dokokin Zamfara tana yunƙurin tsige mataimakin gwamna Mahadi Aliyu

Daga SANUSI MUHAMMAD, Gusau

Majalisar Dokokin jihar Zamfara ta fara wani sabon yunƙurin tsige mataimakin gwamnan jihar Barr. Mahadi Aliyu Muhammad Gusau.

Rahotanni sun nuna cewar, Mataimakin Gwamnan dai ya shafe kusan watanni shida bai je ofis ba inda ya tare a Abuja daga Gusau babban birnin jihar tun lokacin da Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya fice daga PDP ya koma APC mai mulki a ƙasar.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa tuni aka miƙa takardar tsige shugaban majalisar dokokin jihar ga Kakakin Majalisar, Hon. Nasiru Muazu Magarya a safiyar jiya Juma’a domin ɗaukar matakan ƙarshe.

Majiyar mu daga majalisar dokokin ta bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja cewa mataimakin kakakin majalisar kuma shugaban kwamitin majalisar a kan asusun gwamnati, Hon. Musa Bawa ne ya jagoranci ’yan tawagarsa tare da miƙa takardar tsige Mataimakin gwamnan.

Sai dai kakakin, Hon. Nasiru Muazu Magarya bayan karɓar wasiƙar ya ce nan ba da jimawa ba za su duba shawarar dake ƙunshe a cikin wasiƙar tsige mataimakin gwamnan kamar yadda kundin tsarin mulki na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya tanada.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan majalisar dokokin jihar a watan Yulin 2021, sun zargi mataimakin gwamnan na jam’iyyar PDP, tare da ba shi wa’adin sa’o’i 48 da ya gurfana a gaban ta bisa zargin rashin ɗa’a da aka yi masa a hukumance.

Sai dai kuma abin jira a gani shi ne hanyar da majalisar dokokin jihar za ta bi a wannan karon wajen tsige shi.

Blueprint Manhaja ta rahoto cewa rikicin da ke tsakanin mataimakin gwamnan jihar Mahadi Aliyu Gusau da maigidansa gwamna Matawalle ya yi tsami jim kaɗan bayan Gwamna Matawalle ya koma APC ya bar PDP da ta kai su hawa kujerar jihar.